Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Ɗan Takarar Majalisa a 2023 da Wasu, Sun Nemi Sabbin Kudi

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Ɗan Takarar Majalisa a 2023 da Wasu, Sun Nemi Sabbin Kudi

  • Yan bindigan sun yi garkuwa da wasu mutum hudu a yankin Gusau na jihar Zamfara, sun nemi a biya fansa da sabbin takardun kuɗi
  • Wani mazaunin kauyen Kolo da lamarin ya faru, yace suna kokarin haɗa kudin amma maharan suka ce sai da Sabbin kuɗi
  • Miyagu sun yi awon gaba da ɗan takarar majalisar dokokin Imo na APGA amma wasu rahotanni sun ce ya kubuta

'Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane huɗu da ya haɗa namiji, mace da kuma yara biyu a ƙauyen Kolo, ƙaramar hukumar Gusau a jihar Zamfara.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa bayan sace mutanen, yan ta'addan sun nemi a biya kuɗin fansa miliyan N10m kuma sun ƙi karɓan takardun naira na yanzu.

Harin 'yan bindiga.
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Ɗan Takarar Majalisa a 2023 da Wasu, Sun Nemi Sabbin Kudi Hoto: punchng
Asali: UGC

Wani mazaunin yankin, Mohammed Ibrahim, yace daga baya yan fashin dajin sun rage kuɗin zuwa miliyan N5m. Ya ƙara da cewa mutanen ƙauyen na kokarin haɗa kudin don kuɓutar da 'yan uwansu.

Kara karanta wannan

Ana Tsaka da Shan Soyayya, Budurwa Ta Burma Wa Saurayinta Sadiq Ɗahiru Wuka Har Lahira

Mutumin yace:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Yayin da muke kokarin tara kuɗin da suka buƙata, kwatsam suka sake aiko da sabon sakon cewa ba zasu karɓi tsofaffin takardun naira ba. Sun ce zasu rike mutanen har zuwa Disamba da za'a saki sabbin."

Da aka kira mai magana da yawun yan sandan jihar Zamfara, SP Mohammed Shehu, da kwamishinan yaɗa labarai, Ibrahim Dosara, ta wayar salula ba su ɗaga ba.

An sace ɗan takarar majalisa a Imo

A wani cigaban, yan bindiga sun yi garkuwa da ɗan siyasa mamban jam'iyyyar APGA, Nduka Anyanwu, a jihar Imo.

Jaridar ta tattaro cewa Anyanwu, ɗaya daga cikin 'yan takarar majalisar dokokin jihar a jam'iyyar APGA, na tsaka da Kamfe tare da masoyansa lokacin da maharan suka farmakesu, suka yi awon gaba da shi.

Da yake labarta yadda lamarin ya faru, wata majiya tace:

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Fitaccen Malami a Jihar Arewa, Sun Nemi Fansa

"Yan bindigan sun tsayar da jigon siyasan yayin da yake hanyar zuwa karisa wasu shirye-shirye na runfunan zaɓe. Har yanzu bamu san inda suka kai shi ba kuma ba su kira waya ba."

Shin ɗan takarar ya kubuta?

Amma da aka tuntubi shugaban jam'iyyar APGA a jihar Imo, John Iwuala, ya tabbatar da garkuwa da ɗan siyasan amma yace maharan sun sake shi.

Yace, "Eh tabbas an yi garkuwa da ɗan takararmu da safiyar nan amma muna shirin kai rahoto a hukumance sai muka samu labarin masu garkuwan sun sako shi."

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Matashin Malami a Jihar Kwara, Sun Nemi Fansa

Wasu miyagun yan bindiga sun kutsa har cikin gida sun sace wani matashin Malami, ɗan uwansa da kuma ɗansa a wata Anguwa dake gefen Ilorin, babban birnin jihar Kwara.

Mahaifin malamin, sananne mutum a yankin ya yi kira ga mahukunta da masu fatan alkairi su taimaka wa iyalansa wurin kubutar da 'ya'yansa da jika domin babu kuɗin da duka nema.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Abubakar Na Shirin Janyewa Daga Takarara Shugaban Ƙasa? Gaskiya Ta Fito

Asali: Legit.ng

Online view pixel