"Kowa A Jiha Ta Masoyin Buhari Ne": Gwamnan PDP Ya Aika Saƙo Mai Kaɗa Hanta Ga Atiku

"Kowa A Jiha Ta Masoyin Buhari Ne": Gwamnan PDP Ya Aika Saƙo Mai Kaɗa Hanta Ga Atiku

  • Bala Mohammed, gwamnan jihar Bauchi kuma mataimakin shugaban kunguyar kamfen din takarar shugabancin kasa na PDP a arewa maso gabas, ya ce kowa a jiharsa masoyin Buhari ne
  • Gwamnan na PDP ya furta hakan ne yayin kaddamar da aikin hakar danyen man fetur na Kolmani a Bauchi, ranar Talata, inda Shugaba Muhammadu Buhari ya halarta
  • A baya, Mohammed ya yi ikirarin cewa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP na masa zagon kasa a yunkurinsa na zarcewa kan mulki karo na biyu

Bauchi, Bauchi - Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya amsa cewa mutanen jiharsa magoya bayan Shugaba Muhammadu Buhari ne.

Mohammed, wanda daya ne cikin shugabannin PDP ya ce "kowa a jiharsa magoyin bayan Buhari ne" a wurin kaddamar da kamfanin Kolmani Integrated Development Project a jihar Bauchi a ranar Talata, 22 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Matasan Jihar Buhari Sun Fara Zuwa Gida-Gida, Sun Yi Wa Tinubu Alkawarin Kuri'u Miliyan a 2023

Buhari, Mohammed and Atiku
"Kowa A Jiha Ta Masoyin Buhari Ne": Gwamnan PDP Ya Aika Saƙo Mai Kaɗa Hanta Ga Atiku. Hoto: Atiku Abubakar.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sunanyen jihohin arewa da suka shiga jerin jihohin masu samar da man fetur

Legit.ng ta saka ido kan kaddamarwar kai tsaye a shafin Twitter na Channels TV.

Buharim, wanda jagora ne a jam'iyyar APC kuma shugaban kwamitin kamfen din yakin neman zaben Tinubu/Shettima, ya yi murmushi yayin da ya ji kalaman gwamnan Bauchin.

Tare da shugaban kasar a wurin kaddamarwar akwai Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan; direkta janar na kwamitin kamfen din shugaban kasa na APC, Simon Lalong, Ministan sadarwar da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Pantami da wasu.

Taron shine kaddamar da hakar danyen man fetur karon farko a arewacin Najeriya a hukumance, wanda aka gano a iyakan jihohin Bauchi da Gombe duk a arewa maso gabas.

Kara karanta wannan

2023: A Karshe Oshiomhole Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Tinubu Zai Kayar Da Atiku Domin Ya Ci Zaben Shugaban Kasa

Halin da ake ciki a rikicin PDP, Atiku Abubakar, Bala Mohammed, Jihar Bauchi, Zaben 2023

Bala Mohammed, gwamnan jihar Bauchi ya nuna rashin jin dadinsa da halin dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar, na yin watsi da shi.

Idan za a iya tunawa Mohammed ne mataimakin shugaban kwamitin kamfen din shugaban kasa na PDP a zaben 2023 a arewa maso gabas.

Gwamnan ya yi ikirarin Atiku baya goyon bayan tazarcensa a jihar Bauchi kuma bai ziyarce shi ba bayan zaben fidda gwani kamar yadda ya ziyarci sauran yan takara.

Mohammed ya ce saboda bai janye wa Atiku ba yayin zaben fidda gwani, mai fatan zama shugaban kasar bai ji dadi ba.

Gwamnan Bauchi Ya Siffanta Tsohon Shugaban Najeriya Jonathan Da Shugaban Kirki

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya siffanta tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan da shugaba mafi nagarta da Najeriya ta taba yi.

Kara karanta wannan

2023: Ku Yi Hattara Da Peter Obi, Kungiyar Matasan Kirista Ta Aike Da Sako Mai Karfi Ga Yan Najeriya

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da Jonathan ya ziyarce shi a Bauchi don yi masa ta'aziyyar rasuwar dan uwansa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel