Jam’iyyar PDP ta dura Majalisa, ta na so a hana ba Mai ba Buhari shawara kujera a hukumar INEC

Jam’iyyar PDP ta dura Majalisa, ta na so a hana ba Mai ba Buhari shawara kujera a hukumar INEC

  • PDP ta gudanar da zanga-zangar lumana a harabar Majalisar Tarayya a yau
  • Jam’iyyar ta nemi a cire sunan Lauretta Onochie a cikin kwamishinonin INEC
  • Shugabannin PDP sun ce Onochie ba wanda za ta iya adalci a aikin zabe ba ce

Daily Trust ta fitar da rahoto cewa a yau ranar Laraba, 30 ga watan Yuni, 2021, wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP, sun shirya zanga-zanga a majalisar tarayya.

‘Yan jam’iyyar adawar sun gudanar da zanga-zangar lumanar ne domin nuna rashin amincewarsu a kan shirin ba Misis Lauretta Onochie mukami.

Onochie ta na cikin masu taimaka wa shugaban Najeriya wajen harkar yada labarai ta kafafen zamani.

KU KARANTA: Dokar kasa ba ta ba Gwamna Matawalle damar ya tsere daga PDP ba

Lauretta Onochie ba za ta iya yin gaskiya ba - PDP

Shugaban jam’iyyar PDP, Prince Uche Secondus, ya jagoranci masu zanga-zangar zuwa harabar majalisar, ya na kira ga Sanatoci su yi fatali da sunan Onochie.

Prince Uche Secondus ya koka da cewa Lauretta Onochie ba ta dace da kujerar babbar kwamishinar hukumar zabe ba, domin ba za ta iya yin adalci ba.

PDP ta hannun sakatarenta na kasa, Umaru Ibrahim Tsauri, ta rubuta takardar koke zuwa ga shugaban kwamitin INEC a majalisar dattawa, Sanata Kabiru Gaya.

Korafin da PDP ta kai gaban kwamitin Kabiru Gaya

“Jam’iyyarmu ta na ganin akwai muhimmancin mu jawo hankalin kwamitinka, domin aikinmu ne mu fadakar da majalisar tarayya ta yi abin da ya dace a bisa doka.”

KU KARANTA: Shugaba Muhammadu Buhari ba barawo ba ne - Lauretta Onochie

Lauretta Onochie
Lauretta Onochie da Shugaban kasa Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

“Kundin tsarin mulkin 1999 ya haramta wa mutane irinsu Onochie rike mukami a hukumar INEC, domin za ta nuna ra’ayin siyasarta, ta na ma da katin zama 'yar jam’iyya.”

Wasikar ta ce idan aka ba Onochie wannan kujera, an ci amanar damokaradiyya domin kowa ya san ‘yar zafin jam’iyyar APC ce, za ta nuna son kai a wurin aikinta.

The Nation ta tabbatar da wannan rahoto, ta ce an gudanar da zanga-zangar ne dazu da rana.

Kwanakin baya Muhammadu Buhari ya tura sunan Lauretta Onochie zuwa majalisar dattawa, inda ya bukaci a tantance ta a matsayin kwamishinar INEC ta kasa.

Buhari ya gabatar da sunan hadimarsa, da wasu mutane uku dabam a gaban majalisar dattawa domin a tantancesu da nufin su rike wadannan kujeru a hukumar zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel