Yau Laraba Shugaba Buhari Zai Bayyana Samfurin Sabon Kudin Najeriya

Yau Laraba Shugaba Buhari Zai Bayyana Samfurin Sabon Kudin Najeriya

  • Ranar fitar da sabbin takardun Naira ta mats yayinda ake shirin bayyana samufurin ranar Laraba
  • Gwamnan bankin da ke da hakkin fitar da kudin ya ce Shugaban kasa da kansa zai bayyana
  • Rabon da Najeriya ta sauya fasalin kudinta tun ranar 28 ga Febrairu, 2007, shekaru 15 yanzu

Abuja - Gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari zai bayyana samfurin sabon kudin Najeriya 'Naira' yau Laraba, 23 ga Nuwamba, 2023.

Emefiele ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin zaman kwamitin MPC a birnin tarayya Abuja, rahoton ChannelsTV.

Hakazalika ya sanar da cewa an kara alkaluman kudin ruwa daga 15.5% zuwa 16.5%.

Buhari
Yau Laraba Shugaba Buhari Zai Bayyana Samfurin Sabon Kudin Najeriya
Asali: Getty Images

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Mene ne Gaskiyar Lamarin? Bidiyon Sabbin Takardun Naira da Aka Canzawa Fasali Ya Bazu

Mun kawo muku cewa Emefiele a ranar 26 ga Oktoba ya sanar da sauya fasalin takardun Naira N200, N500, da N1000.

Yace za'a fitar da sabbin takardun ranar 15 ga Disamba, 2022 kuma za'a daina amfani da wadanda ke gari yanzu ranar 31 ga Junairu, 2023.

Amma a yau Talata, Emefiele yace gwamnati ta canza shawara, ba za'a jira sai ranar 15 ga Disamba ba saboda Shugaban kasa na bayyanasu ranar Laraba zasu fara yawo.

Dalilan sauya fasalin Naira uku, a cewar shugaba Buhar

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babu ja da baya game da lamarin sauya fasalin takardun kudin Najeriya 'Naira'.

Buhari ya bayyana hakan yayinda yake hira da manema labarai a Landan.

Yace Tattalin arzikin Najeriya zai amfana da wannan abu saboda wadannan dalilai guda uku:

- Hauhawar farashin kaya zai ragu

- Masu hada kudaden jabu zasuyi asara

Kara karanta wannan

Hotuna da bidiyon Wajen Hakar Arzikin Mai Na Farko A Arewa Da Buhari Zai Kaddamar Yau

- Kudaden da yawo a gari zasu ragu

Gwamnan CBN Emefiele Ya Umurci Dukkan Bankuna Su Fara Budewa Ranar Asabar

Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele ya umurci dukkan bankunan dake Najeriya su fara budewa ofishohinsu ranakun Asabar daga yanzu zuwa ranar 31 ga Junairu don mutane su samu damar mayar da kudadensu.

Diraktan Yada Labaran Bankin, Osita Nwasinobi, ne ya sanar da wannan umurni da aka yiwa bankunan.

Ya bayyana hakan ne a wani taron baja kolin CBN da ya gudana ranar Alhamis a Ilori, birnin jihar Kwara.

Nwasinobi ya samu wakilcin mukaddashin Diraktan sadarwan bankin, Akpama Uket.

Asali: Legit.ng

Online view pixel