Hotuna da bidiyon Wajen Hakar Arzikin Mai Na Farko A Arewa Da Buhari Zai Kaddamar Yau

Hotuna da bidiyon Wajen Hakar Arzikin Mai Na Farko A Arewa Da Buhari Zai Kaddamar Yau

  • Komai ya kankama domin kaddamar da wajen hakar arzikin man fetur karo na farko a Arewacin Najeriya
  • Shgaba Muhammadu Buhari da kansa zai kaddamar da wannan rijiyar arzikin mai a Alkaleri
  • Jihohin Gombe da Bauchi yanzu zasu shiga jerin jihohin Najeriya masu arzikin man fetur

A Yau Talata, Shugaba Muhammadu Buhari, zai kaddamar da hakan arzikin man fetur na farko a tarihin Arewacin Najeriya a jihar Bauchi da Gombe.

Wannan hakar arzikin mai da zai kasance a Kolmani (OPL) 809 da 810.

Shekaru biyu da suka gabata aka gani arzikin man fetur a Arewa.

"Bikin fara tonon zai gudana ne ranar Talata, 22 ga watan Nuwamba kuma shugaban kasa da kansa zai halarta tare da yawancin ministocinsa fari da karamin Ministan man fetur, Timipre Sylva," jawabin gwamnati.

Kara karanta wannan

Alkawuran Atiku: Zan yiwa Arewa aiki kamar Abubakar Tafawa Balewa idan na gaji Buhari a 2023

Bahsir
Hotunan Wajen Hakar Arzikin Mai Na Farko A Arewa Da Buhari Zai Kaddamar Yau Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hadimin Shugaba Buhari kan sadarwan zamani, Bashir Ahmed, ya saki hotunan wajen hakar man da Shugaba Buhari zai kaddamar yau.

Yace:

"Da fatan kun waye gari lafiya daga OPL) 810, Kolami, Alkaleri a jihar Bauchi. Rijiyar hakar man farko na Arewa maso gabashin Najeriya. Mun gode Baba."

Kalli hotunan wajen:

Kalli bidiyon:

Asali: Legit.ng

Online view pixel