Maganar Sauya Fasalin Naira, Babu Gudu Babu Ja Da Baya: Shugaba Buhari

Maganar Sauya Fasalin Naira, Babu Gudu Babu Ja Da Baya: Shugaba Buhari

  • A ziyarasa ta Landan, Shugaba Buhari ya sake bayyana goyon bayansa ga sauya fasalin Naira
  • Shugaba Buhari ya bayyana amfani uku da sauya fasalin zai yiwa tattalin arzikin Najeriya
  • Ranar 15 ga watan Disamba za'a fitar da sabbin samfurin N200, N500, N1000 kuma za'a daina karban tsoho ranar 31 ga Junairu

Landan - Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babu ja da baya game da lamarin sauya fasalin takardun kudin Najeriya 'Naira' da ake shirin yi a karshen shekarar nan.

Shugaban kasan ya bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya zai amfana da wannan abu saboda hauhawar farashin zai ragu, masu had akudaden jabu zasuyi asara kuma kudaden da yawo a gari zasu ragu.

Buhari ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin hira da manema labarai jim kadan bayan ganawarsa da Sarkin Birtaniya, Charles III a Buckingham Palace, London, rahoton AIT.

Kara karanta wannan

Yayin da Yake Kasar Waje, Buhari Ya yi Hasashen Yadda Zaben 2023 Zai Kasance

Ya kara da cewa babu wanda za'a bari yayi amfani da kudi wajen daukan nauyin yan bangan siyasa da kuma saya kuri'u lokacin zabe, riwayar PMNews.

Buhari
Maganar Sauya Fasalin Naira, Babu Gudu Babu Ja Da Baya: Shugaba Buhari Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaba Buhari yace:

"Sauyin nan da za'a yi, na san kudade da yawa zasu fuskanci matsala amma lokacin da aka bada daga Oktoba ne zuwa Disamba."
"Watanni uku sun isa amfani da duka kudin da kake da su, ka kaisu banki. Saboda haka ban san dalilin da ya sa mutane ke korafi ba. Babu Gudu, babu ja da baya."

Sauyin Fasalin Naira

Babban bankin Najeriya CBN a watan Oktoba ya sanar da cewa ana shirin sauya kudin N200, 500 da 1000.

Shugaban bankin, Godwin Emefiele, ya ce za;a fara sauyin ne ranar Alhamis, 15 ga watan Disamba, 2022.

Yace daga ranar 31 ga Junairu, 2023 takardun 100, 200, da 500 da ake amfani da su zasu zama wofi.

Kara karanta wannan

Ku yi hakuri: Gwamnan da ya muzanta Fulani ya kira su 'yan ta'adda ya nemi gafararsu

Ina tare da gwamnan CBN

Bayan kwanaki da sanarwan, Shugaba buhari ya bayyana goyon bayansa ga sauya fasalin Nairan.

Wannan ya biyo bayan jawabin Ministar Kudi, Zainab Shamsuna, inda ta bayyana cewa ba da saninta aka yi tsarin sauya fasalin ba.

Tace yadda kowa ya samu labari a talabijin itama haka ta samu labari.

Tace wannan abu na da illa ga tattalin arzikin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel