Bidiyon Tsohuwa Mai Shekaru 53 ta Koma Budurwa Sharaf Bayan Kwalliya Ya Gigita Jama’a

Bidiyon Tsohuwa Mai Shekaru 53 ta Koma Budurwa Sharaf Bayan Kwalliya Ya Gigita Jama’a

  • Wata budurwa mai kwalliya mai suna Sherry Williams ta yadu a yanar gizo bayan bayyana bidiyon daya daga cikin kwalliyar da tayi
  • Tsohuwa ce mai shekaru 53 wacce aka canzawa kamanni baki daya tare da tayar mata da komada inda ta koma budurwa danya sharaf
  • Mutane da yawa sun garzaya sashen tsokaci inda suka dinga bayyana ra’ayoyinsu game da bidiyon kwalliyar da ta fitar

Babu shakka idan aka ce kwalliya, dole mutane masu tarin yawa su hango zancen dabo wanda kuma ba kowa bane Allah ke ba baiwar.

Bidiyon kwalliyar tsohuwa
Bidiyon Tsohuwa Mai Shekaru 53 ta Koma Budurwa Sharaf Bayan Kwalliya Ya Gigita Jama’a. Hoto daga @kammyismymotivation
Asali: Instagram

Toh, wannan mai shekaru 53 za a iya danganta ta da mai sihirin kwalliya wacce sauyawar da ake yi bayan ta kammala zane fuska take barin dubban jama’a da mamaki.

A bidiyon TikTok da aka wallafa a shafin Instagram din, an ganta tana tsara kwalliya kuma cike da kwarewa da son sauya halitta wanda daga bisani ya koma abun mamaki.

A yayin da ta fara duba shekaru da farko tunda tsufa ya bayyana, daga bisani ta koma danya sharaf tamkar wata budurwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalla bidiyon:

Ma’abota amfani da soshiyal midiya sun yi martani game da kwalliyar

Bidiyon da tuni ya yadu a yanar gizo, ya bar mutane suna yabawa yayin da wasu kuma suka bude baki cike da mamaki.

Ga wasu daga cikin tsokaci:

Obaksolo:

“Kai, baki kuwa amma fa tayi kyau.”

Gylliananthonette:

“Shekaru 53 amma ta koma kamar 33. Baki baya bayar da kunya.”

Adorable_barbiiee:

“A gaskiya zan fara kwalliya saboda tana kara wa mutane kyau.”

Chioma4eva:

“Wani ya taba fada min cewa kamata yayi a dinga kama mata da suka yi kwalliya kan basaja. Da na tambaye shi wa suka yi wa basaja, sai yayi shiru tare da fadawa tunani. Don Allah ku tsahirtawa mata, kamata yayi ku dinga biyanmu kan kyau da muke yi muna faranta muku rai.”

Adaikwerre:

“A wannan rayuwar kawai gyara kan ka. Mu din ma muna da kyau a yadda muke. Ban taba tsammanin hakan ba.”

Lingeriebytemmy:

“Ta yaya tsohuwa zata canza ta koma budurwa haka?”

Ba wannan bane karo na farko

Masu kwalliya sun saba bai wa jama’a mamaki inda suke sauya halittar wadanda suke mika fuskokinsu domin su yi tsaf.

Maza kan kira lamarin da a cuci maza yayin da mata ke kallonshi a iya gayu da kwalliya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel