Na Fasa: Ana Gab Da Daurin Aure, Ango Yace Ya Fasa Bayan Gano Amaryar Na Da 'Yaya 2

Na Fasa: Ana Gab Da Daurin Aure, Ango Yace Ya Fasa Bayan Gano Amaryar Na Da 'Yaya 2

  • Wani sabon Ango ya fusata matuka bayan gano cewa matar da yake shirin aure na da yara biyu
  • A bidiyon da ya yadu a kafafen sada zumunta, Ango ya ce ya fasa auren gaba daya a bainar jama'a
  • Yan Najeriya a soshiyal Midiya sun bayyana mabanbantan ra'ayi kan bidiyon; yayinda wasu ke ce ya yafe mata, wasu sun ce yayi daidai

Ana gab da daurawa, Wani Ango ya dakatar da daurin aurensa bayan bankado wani abin mamaki tattare da Amaryar da yake shirin aure.

Mutumin a filin bikin ya gano cewa Amaryar ta taba haihuwa har sau biyu wa wani mutumi daban.

bride of 2
Na Fasa: Ana Gab Da Daurin Aure, Ango Yace Ya Fasa Bayan Gano Amaryar Na Da 'Yaya 2 Hoto: @Enywealth_1
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A bidiyon mai ban takaici, mutumin ya bayyana bacin ransa kuma ya soke auren gaba daya a gaban yan'uwa da abokan arziki.

Kara karanta wannan

Hoton ‘dan Najeriya Ya Kai $500k Banki Domin Adanawa ya Ba Jama’a Mamaki

Mahalarta wajen sun yi iyakan kokarin bashi hakuri amma yace sam.

Ya bukaci iyalan Amarya su dawo masa da kudin sadakin da ya biya.

Kalli ra'ayoyin yan Najeriya da bidiyon:

Zubairu M Zubairu yace:

"Indai ta hanyar lalle ta samesu ae babu damuwa a haka"

Maryama Y Ibrahim tace:

"Allah ya kyauta daman ba sonta yakeyiba,alamun tana da kwai da yawa a cikinta"

Adams Jimeta:

Hhhhh kai amma wannan hegiya ceh amma meyasa baiyi bincike ba

Mariya M Aliyu:

"Gaskiya gwara da ya fasa, wannan zata iya cin amanarsa, tunda har ta 6oye sirrinta irin wannan"

Idris Maikusa Wakilin BabanYaba yace:

"Kansa yayiwa ai, dacan baisan tanada ƴaƴan ba?
Allah ya canza miki da mafiyinsa"

Al-Mustapha Yusuf Baba

Gaskiya ya dace tun kafin yanzu yasan ta haifu

Muhammad Sani Umar:

Shiyasa bayyana gaskiya shine komai, data fadi gaskiya shikenan da hakan bata faruba.

Aleeyu Amiin

Kara karanta wannan

Rigimar PDP: Tsagin Gwamna Wike G5 Sun Gindaya Sharudda a Sabon Shirin Sulhu da Su Atiku

Ae kam dole kana kurin ka sai Tear leader ashe London use ne

Aliyu Aminu Mohammed:

Toh dama shi idonsa baya gani ne..?
Shi Bai san budurwa ba da wadda ta goguba..

Asali: Legit.ng

Online view pixel