Shugaba Buhari Ya Ce Ya Kamata Malaman Jami'a da Sauran Kungiyoyin Kwadago Su Daina Yajin Aiki

Shugaba Buhari Ya Ce Ya Kamata Malaman Jami'a da Sauran Kungiyoyin Kwadago Su Daina Yajin Aiki

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sako mai zafi ga malaman jami’a da duk wadanda ke Shirin shiga yajin a nan gaba
  • Shugaba Buhari ya ce ya kamata kungiyoyi suke rungumar sulhu da gwamnati sabanin tafiya yajin aiki mara ma’ana
  • Kungiyar malaman jami’a ta ASUU na ci gaba da kai ruwa da gwamnatin Najeriya kan batun da ya shafi albashi

Ibadan, jihar Oyo - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shawarci kungiyar malaman jami’o’i da sauran kungiyoyin ma’aikata da su rungumi sulhu da gwamnati tare da gudun yajin a matsayin hanyar neman a biya musu bukatu.

Buhari ya bayyana hakan ne a taro na 74 na yaye dalibai a jami’ar Ibadan a ranar Alhamis 17 ga watan Nuwamba, PM News ta ruwaito.

Shugaba Buhari ya samu wakilcin farfesa Abubakar Rasheed ne a taron, wanda shine babban sakataren hukumar jami’o’i ta kasa (NUC).

Kara karanta wannan

Atiku Ya Bayyana Muhimmin Abunda Gwamnatinsa Zata Maida Hankali Bayan Lashe Zaben 2023

Buhari ya magantu kan batun yajin aiki
Shugaba Buhari ya ce ya kamata malaman jami'a su daina yajin aiki | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Buhari ya kuma yaba da kokarin gudunarwar jami’ar Ibadan bisa kare martabar jami’ar a idon duniya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma yaba da kokarin jami’ar wajen yaye daliban sama da digiri na farko masu nagarta da ke sanya kasa alfahari a ciki da wajen kasar nan.

Yajin aiki na taba tattalin arziki da nagartar karatu, inji Buhari

Buhari ya kuma bayyana cewa, akwai bukatar ladabtarwa da tabbatar da halaye na gari a dukkan jami’o’in kasar nan domin ciyar da kasar nan gaba.

Ya shaida cewa, ya kadu da yadda kungiyoyin jami’o’i a kasar nan suka daura damarar fada da gwamnati a wannan shekara ta 2022, People Gazette ta tattaro.

Shugaban ya ce sabanin da ke tsakanin gwamnati da malaman na da matukar tasiri mai muni ga tattalin arzikin kasar nan, musamman duba da yadda hakan ke shafar zangon karatun dalibai.

Kara karanta wannan

Gasar 2023: Za a Yi Gasar Karatun Al-Qur'ani Na Kasa, An Fadi Jihar Da Za Ta Karbi Bakuncin Taron

Ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin gwamnatin Najeriya da kungiyar malaman jami'a ta ASUU kan albashin malamai.

Gwamnatin Buhari ta ce ba za ta biya ASUU albashin aikin da bata yi ba

A wani labarin, gwamnatin Najeriya ta ce ba za ta biya albashi ga malaman jami'an da basu yi aiki ba na tsawon watanni.

An warware rikicin ASUU da gwamnati na wucin gadi, amma lamarin ya sake tashi tun bayan da aka biya ASUU rabin albashi.

Wannan batu na fitowa ne daga bakin ministan ilimi, Malam Adamu Adamu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.