Kungiyoyi Sun Yi Gangami a Kaduna, Sun Yi Wa Tinubu Alkawarin Kuri'u Miliyan Hudu a 2023

Kungiyoyi Sun Yi Gangami a Kaduna, Sun Yi Wa Tinubu Alkawarin Kuri'u Miliyan Hudu a 2023

  • Wasu kungiyoyin goyon bayan APC a jihar Kaduna sun dauki alkawarin kawowa Asiwaju Bola Tinubu kuri’u miliyan hudu a 2023
  • Kungiyoyin wadanda suka gudanar da wani gagarumin gangami a jihar don tallata Tinubu sun ce yana da abun da ake bukata don shugabantar Najeriya
  • Sun kuma sha alwashin aikata irin haka ga duk wasu yan takarar jam'iyyar mai mulki a jihar Kaduna daga sama har kasa

Kaduna - Kungiyar yada muradun takarar Tinubu mai suna BAT-PAM ta gudanar da wani gangami a ranar Lahadi a jihar Kaduna don goyon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Kungiyar ta ce zata kawowa tsohon gwamnan na jihar Lagas kuri’u miliyan hudu a babban zaben 2023, jaridar The Nation ta rahoto.

Bola Tinubu
Kungiyoyi Sun Yi Gangami a Kaduna, Sun Yi Wa Tinubu Alƙawarin Kuri'u Miliyan Hudu a 2023 Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

An shirya gangamin ne tare da hadin gwiwar wata kungiyar mai suna 100 Per Cent Focus Movement, don wayar da kai da kuma karfafawa yan Najeriya gwiwar shiga tsarin zabe da kuma zabar Tinubu a shekara mai zuwa.

Kara karanta wannan

2023: Kada Yan Najeriya Su Cire Rai, APC Zata Kawo Canjin da Suke Bukata, Tinubu

Tinubu da Shettima sun cancanci shugabancin Najeriya

Jagoran kungiyar BAT-PAM, Mista Abdulhakeem Ajeseku, ya fadama manema labarai a wajen gangamin cewa Tinubu da abokin takararsa, Sanata Kashim Shettima suna da abubuwan bukata don gudanar da harkokin kasar idan aka zabe su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya bayyana cewa sun yi kuma an gani a kasa sannan su mutane ne da ke mayar da hankali wajen ganin sakamako mai kyau kan duk abun da suka sanya a gaba.

Ajaseku ya ce:

“Za mu baiwa Tinubu da Shettima kuri’un da baza su gaza guda miliyan hudu zuwa miliyan biyar ba.
“Za mu kawo irin haka ga Sanata Uba Sani, dan takararmu na gwamna, haka yan takararmu na sanata, Alhaji Muhammad Sani Dattijo zuwa Bello El-Rufai."

A nashi bangaren, Malam Abubakar Tanimu, jagoran kungiyar 100 Per Cent Focus Movement a yankin arewa maso yamma ya ce nazarin kungiyar kan Tinubu da Shettima na da kyau don haka suka basu goyon baya.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP Da Suka Bayar Da Sharudda A Bainar Jama'a Kafin Yi Wa Atiku Aiki A Jihohinsu

Tanimu ya ce kungiyar na aiki tare da sauran kungiyoyi da dama ciki harda Tinubu Vanguard da kungiyar matasan APC wanda duk matasa ne suka cika su.

Ya kara da cewar:

“Muna ta wayar da kan matasa wajen cimma manufa daya na nasarar dan takararmu.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel