Babbar Kotun Daukaka Kara Ta Shirya Yanke Hukunci Kan Zaben Fidda Gwanin Jam'iyyar APC

Babbar Kotun Daukaka Kara Ta Shirya Yanke Hukunci Kan Zaben Fidda Gwanin Jam'iyyar APC

  • Tun Bayan Zaben fidda gwani na Gwamnan Jihar Adamawa a jam'iyyar APC ake samun Sabani
  • Binani Ta ajiye mukamin zama ko'odinetan zaben Tinubu a Jihar Adamawa Bayan da turka-turka ta mamaye jam'iyyar a jihar
  • Mallam Nuhu Ribadu dai ya kalubalanci zaben, inda yake cewa an aringido da cushe a zaben fidda gwanin.

Adamawa: Kotun daukaka kara ta shirya yanke hukunci kan karar da wadda ta lashe zaben fidda gwani na gwamna a jam’iyyar APC na jihar Adamawa, Sanata Aishatu Binani ta shigar.

In ba’a manta ba dai Babban Alkalin Kotun Daukaka Kara da ke zaman ta a Yola, Mai shari’a Abdulaziz Anka ya soke zaben fidda gwanin a watan Oktoban da ya gabata bisa ga korafin da aka shigar na magudi da kuma cushen kuri’u

Kara karanta wannan

Kotu ta Hana APC Sakat, An Sake Ruguza Zaben Tsaida Gwanin da Aka Yi a Taraba

Tsohon Shugaban Hukumar Ta’annati da Kare Dukiyar Kasa Mallam Nuhu Ribadu ne ya shigar da karar yana kalubalantar nasarar Binani.

Babbar kotun tarayya ta umurci Binani da ta daina bayyana kanta a matsayin yar takarar gwamna a jam’iyyar APC yayin da kotun ta soke zaben.

Kotun daukaka kara wadda masu shari’a a Teni Yusuf Hassan, M.O Bolaji da James Abundaga ta kammala shirin yanke hukuncin bayan da suka saurari hujojin masu shigar da kara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Binani
Babbar Kotun Daukaka Kara Tayi Mi-Ara-Koma Baya Kan Hukuncin Zaben Fidda Gwanin Jam'iyyar APC Hoto: UCG
Asali: UGC

Babban Lauyan Binani, Cif Akin Olujimi (SAN), wanda ya jagoranci wasu Lauyoyi masu mukamin SAN su shida da kananan lauyoyi 12 ya bukaci kotun daukaka kara da ta yi watsi da hukuncin da kotun ta yanke tare da tabbatarwa Binani matsayinta da kuma amince mata ci gaba da gudanar da.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kotun Daukaka Kara ta Kori Akpabio Daga Takarar Sanata

Duk da haka lauyoyin Ribadu, I.K. Bawa (SAN), wanda ya bayyana tare da S.T Ologunorisa (SAN) ya bukaci kotun da ta bada umarnin sake gudanar da zabe, yana mai cewa karamar kotun ta yi kuskure a doka bayan ta ki amincewa da sake sabon zabe ko da ta kafa shari’ar zaben da ya saba wa doka.

Sanata Binani Ta Sauka daga Shugabancin Kwamitin Yakin Zaben Tinubu na Adamawa

A takardar da ta saka hannu da kanta a kai, ta bayyana cewa ta sauka ne har zuwa lokacin da kotun daukaka kara zata yanke hukunci kan karar da ta mika ta hana ta takarar kujerar gwamnan jihar a zabe mai zuwa.

Wata majiya kusa da Binani ta sanar da Daily Trust cewa, ta yanke hukuncin sauka daga mukamin a ranar Alhamis bayan ta fusata da kalaman da wani mamban jam’iyyar yayi a kan wasu manyan masu ruwa da tsaki da suka hada da tsohon Gwamnan jihar Murtala Nyako.

Kara karanta wannan

Sabuwar Baraka: Sanatan PDP Ya Aje Atiku, Ya Yaba Wa Bola Tinubu Kan Wani Muhimmin Abu

Asali: Legit.ng

Online view pixel