Donal Trump Ya Bayyana Aniyarsa Ta Tsayawa Takarar Shugaban Kasa A Zaben 2024

Donal Trump Ya Bayyana Aniyarsa Ta Tsayawa Takarar Shugaban Kasa A Zaben 2024

  • A shekarar 2020 ne dai aka kada Trump a matsayin shugaban kasar Amurka, sabida yadda aka zargi gwamnatinsa da tirka-tirka
  • Kamfanin Twitter mai dai, sun dakatar da Trump daga wallafa a shafin na tsawon shekara guda
  • Yar gidan Donald Trump ta auri wani dan Nigeria, a satin da ya gabata, dan Nigeria dai hafafen labenon, wanda iyayensa kuma suke haifaffun Jihar Legas

Amurka: Donald Trump ya bayyana aniyarsa ta sake shiga fadar gwamnatin White House, baya da zaben Jin ra'ayin tsakiyar gwamnati ya nuna yadda jama'a suka kosa dan gane da wasu batu.

Trump ya kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa a hukumance na shekarar 2024, inda ya mika takarda ga hukumar zaben Amurka inda ya ayyana kansa a matsayin dan takarar shugaban kasa tare da kafa sabon kwamitin yakin neman zabe.

Kara karanta wannan

Cristiano Ronaldo ya Dauke ‘Ya ‘yansa daga Manchester, Kulob Sun Maida Masa Martani

Trump
Donal Trump Ya Bayyana Aniyarsa Ta Tsayawa Takarar Shugaban Kasa A Zaben 2024 Hoto: MANDEL NGAN / AFP
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ana sa ran Trump zai gabatar da jawabi da yamma a kulob dinsa na Florida, Mar-a-Lago. kamar Yadda Vangurad ta rawaito

“Dawowar Martabar Amurka yanzu ya fara," in ji tsohon shugaban na Amurka, mai shekaru 76 a duniya, ya fadawa daruruwan magoya bayansa da suka taru a wani dakin shakatawarsa a gidansa na Mar-a-Lago a Florida.

Kuri’a ce za ta bambanta mu da su sosai. Shin Kuna shiri?"

Trump ya ce yayin da yake bayani

Wannan ba yakin neman zabe na bane, yakin neman zaben mu ne duka"

Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa ya bayar da rahoton cewa, ana ganin ayyana takarar Trump ba zata rasa nasaba da yadda yake so a soke hukuncin da akai masa ba, da kuma danne duk ƴan jam'iyyarsa da suke san fitowa takara.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya yi babban kamu, an daura aurensa da diyar tsohon shugaban Amurka Trump

Yawancin abokan takarar trump a zabne 2024 suna zagayawa, ana ganin babban cikinsu shine gwamnan Florida Ron DeSantis, wanda ya yi nasara a zaben jin ra'ayin jama'a.

Trump, wanda ya sha kaye a zaben 2020 a hannun jam'iyyar Democrat ta Joe Biden bayan da majalisar wakilai ta tsige shi har sau biyu, ya kaddamar da takararsa ta neman shugabancin kasar da masu bukata ta musamman.

Wasu laifukan da ake zargin trump dai sun hada da zargin zamba da sa danginsa a gwamnati, da rawar da ya taka a harin da aka kai a Majalisar Dokokin Amurka a bara, da yunkurinsa na soke zaben 2020, da kuma bayanan sirri da ya fijtar a Mar-a-Lago.

Da Trump a yanzu ya zama dan takara da aka ayyana, mai yiwuwa a tilastawa babban lauyan Biden, Merrick Garland, ya nada wani lauya na musamman don ci gaba da binciken tsohon shugaban kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel