Diyar Trump Ta Auri Wani Saurayi Dan Najeriya a Florida

Diyar Trump Ta Auri Wani Saurayi Dan Najeriya a Florida

  • A yau dai gidan tsohon shugaban kasan Amurka, Donald Trump ya cika da farin ciki yayin da ya aurar da diyarsa
  • Wani dan Najeriya ya angwance da diyar tsohon shugaban kasar Amurka a birnin Florida na kasa ta Amurka
  • An ga dandazon masoya da suka halarci wannan biki mai dimbin tarihi, an yada hotuna masu ban sha'awa

Florida, Amurka - Tiffany Trump, diyar tsohon shugaban kasar Amuka, Donald Trump ta amarce da angonta dan Najeriya, Michael Boulos ranar Lahadi.

An daura auren ne Mar-a-Lago a yankin Palm Beach na birnin Florida tare da halartar Donald Trump da matarsa Melania, The Guardian ta ruwaito.

Boulus, wanda aka rena a Legas ya kasance surkin kasar Lebanon da Faransa. An ce ya dawo Najeriya ne tun yana karami, inda harkar kasuwancin iyayensa yake a lokacin.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Ya Birne Ɗansa, Manyan Ƴan Siyasa Sun Halarci Jana'izar Don Yin Bankwana

Ya yi karatu a makarantar Amurka ta kasa da kasa da ke Legas.

An daura auren Bolous da Tiffany
Diyar Trump Ta Auri Wani Saurayi Dan Najeriya a Florida | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Boulos da ne ga Massad, babban shugaban kamfanin SCOA Nigeria, mahaifiyarsa Sarah kuwa ita ce ta assasa Society for the Performing Arts in Nigeria.

Boulous ya kuma yi karatu a jami'ar City da ke birnin Landan inda ya hadu amaryarsa Tiffany da ke karatu a Geogetown.

Yadda aka yi baikon Tiffanu da Boulus

An yi baikon Tiffany da Boulus ne a ranar 19 ga watan Janairun 2021 a gidan gwamnatin White House na Amurka, sa'o'i kadan kafin karshen wa'adin mulkin Trump, Punch ta tataro.

An yi ta cece-kucen cewa, Boulus ya ba Tiffany lu'u-lu'un da ya siya daga dubai mai darajar akalla dalar Amuka miliyan 1.2.

A yau dai an daura aure, kuma jim kadan bayan ayyana su mata da miji, mutane da dama suka shiga shagali tare da rawa da ma'auratan.

Kara karanta wannan

Ana Zargin Jonathan da Tunzura Gwamnonin PDP 5 Su Juyawa Atiku Abubakar Baya

Yaron ofis ya auri shugabar kamfani

A wani labarin kuma, kun ji cewa, wani dan Najeriya ya yi karfin hali, ya nemi auren wata shugabar kamfanin da ya sami aiki.

A wani lamari mai ban sha'awa, ma'auratan biyu suna rayuwarsu mai dadi kamar yadda suka bayyana.

Mutane da dama sun yi martani, sun taya wadannan ma'aurata murna tare da fatan alheri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel