Cristiano Ronaldo ya Dauke ‘Ya ‘yansa daga Manchester, Kulob Sun Maida Masa Martani

Cristiano Ronaldo ya Dauke ‘Ya ‘yansa daga Manchester, Kulob Sun Maida Masa Martani

  • Manchester United ta yi gajeren martani a shafinta biyo bayan wata hira da aka yi da Cristiano Ronaldo
  • Kungiyar Ingilar tace za ta bada cikakken amsa nan gaba, tace abin da ke gabanta shi ne kakar shekarar nan
  • Ana rade-radin shi kuma ‘dan wasan ya kai ‘ya ‘yansa makaranta a Portugal, alamun zai bar Ingila

Manchester - Alamu na nuna kungiyar Manchester United ba ta ji dadin hirar da Cristiano Ronaldo ya yi da Piers Morgan a karshen makon jiya ba.

Jaridar 90min tace kalaman da suka fito daga bakin ‘dan wasan ba suyi wa Manchester United dadi ba, musamman ganin cewa shi tauraro ne.

Masu kulob din ba su ji dadin yadda abubuwa suke tafiya ba, sun bukaci shugaban kungiyar, Richard Arnold ya yi maza ya shawo kan wannan lamari.

Kara karanta wannan

An yaudare ni: Ronaldo Ya yi Kaca-kaca da Kungiyarsa da Kocin Man Utd a Hira Mai Zafi

Ana haka sai ga jawabi daga Manchester United wanda aka fitar jim kadan bayan babatun Ronaldo. Jawabin ya fito ne a shafin yanar gizon kungiyar.

Jawabin Manchester United

"Manchester United tana ankare da tattaunawa da ‘yan jarida da Cristiano Ronaldo ya yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kungiyar za ta maida martani bayan ta duba lamarin da kyau. Manufarmu ita ce shiryawa ragowar zangon kakar wasan shekarar nan.
Za mu cigaba da kokarin samun hadin-kai tsakanin ‘yan wasa, masu horaswa, ma’aikata da magoya-baya."
Cristiano Ronaldo
Ronaldo da Iyalinsa Hoto: www.thesun.co.uk
Asali: UGC

Iyali za su koma Lisbon?

Ana haka sai ga rahoto daga SAPO Desporto cewa Ronaldo mai shekara 37 ya fara shirin komawa gida domin cigaba da buga kwallo a kasarsa.

Jaridar tace ‘dan wasan ya sa ‘ya ‘yansa a wata makaranta, Saint Julians College da ke Carcavelos. Makarantar tana aiki da tsarin ilmin Birtaniya.

Kara karanta wannan

Hotunan Matashin da Ya Kera Masallacin Karamin Masallacin Ka’aba a Borno Ya Birge Jama’a

Baya ga haka, ana tunanin ‘dan wasan na kasar Portugal ya saye wani katafaren gida Cascais, kuma ya dauki hayar wadanda za su rika masa aiki.

Burin Ronaldo da mahaifiyarsa, Dolores Aveiro shi ne ya koma wasa a gida kafin ya yi ritaya. Sai dai babu alamun cewa ya shirya ajiye kwallo a yanzu.

An yaudare ni - CR7

An samu rahoto Cristiano Ronaldo ya yi ikirarin abubuwa ba su tafiya daidai a kulob din tun da Sir Alex Ferguson ya ajiye aikin horaswa a kakar 2013.

Tsohon 'dan wasan na Real Madrid ya kuma ce bai ganin girman kocinsa, Eric Ten Haag, sannan ya dura kan Wayne Rooney saboda yana sukarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel