‘Yan Bindiga Sun Sheke Dan Sa-kai Da Wasu Mutane 4 a Benue

‘Yan Bindiga Sun Sheke Dan Sa-kai Da Wasu Mutane 4 a Benue

  • 'Yan bindiga sun harbe wani jami'in kungiyar sa-kai da wasu mutane hudu a kauyen Peva a jihar Benue
  • Maharan na zargin dan sa-kan mai suna Oliver da kaiwa jami'an tsaro kwarmato kan ayyukansa don haka suka dungi bibiyarsa
  • Rundunar yan sandan jihar Benue ta tabbatar da faruwa al'amarin, inda tace bata samu cikakken bayani ba tukuna

Benue - Rahotanni sun kawo cewa wasu tsagerun yan bindiga sun kashe mutane biyar a kauten Peva da ke karamar hukumar Katsina-Ala a jihar Benue.

Mazauna yankin sun ce kauyen da abun ya shafa ya kasance Katsina-Ala wanda ke iyaka da garuruwa a karamar hukumar Takum na jihar Taraba, Daily Trust ta rahoto.

Yan bindiga
‘Yan Bindiga Sun Sheke Dan Sa-kai Da Wasu Mutane 4 a Benue Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Sun bayyana wadanda aka kashe da suka hada da dan sa-kai daya da kuma wasu mutane hudu. Sun kuma rasa ransu ne bayan yan bindigar sun harbe su a wani kasuwa da ke yankin.

Kara karanta wannan

Soyayya Ruwan Zuma, Yadda Wata Budurwa Ta Fada Tekun Lagas Akan Saurayi

Yan bindigar sun yi nufin kai harin ne a kan dan sa-kan

Wani mazaunin kauyen mai suna Antavee ya bayyawa jaridar ta wayar tarho cewa mai yiwuwa yan bindigar sun bi sahun dan sa-kan ne zuwa wata mashaya a kasuwar kan zargin baiwa jami’an tsaro bayanai a kan ayyukansu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

“Lamarin ya afku a kauyen Peva da ke iyaka da jihar Taraba ta Katsina Ala. Yan bindigar sun harbe wani jami’in kungiyar sa-kai mai suna Oliver tare da wasu hudu.
“Mun ji cewa yan bindigar sun dade suna bibiyarsa saboda suna zarginsa da kaiwa jami’an tsaro kwarmato a yankin.
“Ana ganin Oliver ne wanda yan bindigar suka so farmaka. Yan bindigar da yawansu ya kai biyar sun isa wata mashaya a kasuwar, inda Oliver ke tare da wasu mutane hudu, a cikin mota mai bakin gilashi.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wasu Fitattun Malamai Biyu a Jihar Arewa

“Ranar cin kasuwa ne kuma da yan bindigar suka hango shi sai suka bude masa wuta tare da sauram mutane da ke mashayar sannan suka yi nasarar kashe shi da wasu hudu. Mutane da dama sun jikkata kuma suna samun kulawa a asibiti. Sai dai kuma yan bindigar sun tsere.”

Rundunar yan sandan Benue ta yi martani

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa jami’ar hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar, SP Catherine Anene wacce ta tabbatar da lamarin ta ce bata samu cikakken bayanin abun da ya faru ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel