Kowa da Ajalinsa: Wasu Daliban Jami'a Su Biyu Sun Rasu a Daki

Kowa da Ajalinsa: Wasu Daliban Jami'a Su Biyu Sun Rasu a Daki

  • Wasu ɗaliban jami'a biyu a jihar Abiya sun rasa rayuwarsu a ɗakin kwanansu dake a wajen makaranta
  • Bayanai sun nuna cewa da yuwuwar guba aka zuba musu a abinci sabida yanayin da aka ga gawarsu da safe
  • Hukumar 'yan sanda tace jami'anta sun ɗauki gwarwakinsu domin gwaji kuma sun kaddamar da bincike

Abia - An wayi gari cikin jimami a jami'ar koyar da ayyukan Noma da kiwo, Michael Okpara University of Agriculture da ke Umudike jihar Abia bayan gano gawar wasu ɗalibai biyu a ɗakinsu.

Jaridar Premium Times ta tattaro cewa ɗaliban biyu, Victor da kuma Chinonso Edeh wanda aka fi sani da Decency suna shekara ta biyu ne a karatunsu kuma suna rayuwa a ɗaki ɗaya a wajen Makaranta.

Jami'ar noma a jihar Abiya.
Kowa da Ajalinsa: Wasu Daliban Jami'a Su Biyu Sun Rasu a Daki Hoto: premiumtimesng
Asali: UGC

An ce Mista Edeh na rike da wani muƙami a ƙungiyar ɗaliban Department ɗinsu kuma yana neman a sake zaɓensa ya cigaba da mulki. An tsara gudanar da zaɓen mako mai zuwa.

Kara karanta wannan

2023: Bayanai Sun Fito, Abinda Gwamnan Bauchi Ya Faɗa Wa Ortom Kan Kalaman Fulani da Atiku

Ɗaliban sun mutu ne bayan cin wani Abinci da Ɗan Acaba, wanda ba'a san ko waye ba ya kawo musu ranar Jumu'a.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bayanai sun nuna cewa bayan gari ya waye shiru basu buɗe ƙofa ba, abokan zama suka ɓalle kofar kana suka ci karo da gawarwakinsu.

Wata majiya daga jami'ar tace Victor ya yi aman jini yayin da aka ga wani farin abu a hancin Edeh, alamun da suka haddasa jita-jitar cewa guba aka sanya musu.

Wani Bidiyo dake yawo a Facebook ya nuna gawar ɗaliban biyu kwance da ɗakin kwanansu. Gawar Edeh na kan gado, Victor kuma na kwance a ƙasan Simintin ɗaki.

"Wani ne ya zuba musu guba, yanzu dai sun mutu baki ɗaya," Wata muryar mace ta faɗa a Bidiyon da ake yaɗawa.

Wane mataki hukumomi suka ɗauka?

Kara karanta wannan

2023: Wasu Daga Cikin Gwamnonin Tsagin Wike Na Shirin Yaudararsa, Zasu Koma Bayan Atiku

Kakakin jami'ar, Adanma Odefa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yace basu da masaniyar wani ɗan Acaba ya kaiwa mamatan abinci, "Abinda muka sani an tsinci gawar ɗalibai a ɗakin kwanansu."

Ya ƙara da cewa jami'an 'yan sanda sun ɗauki gawarwakin kuma tuni hukumar makaranta ta sanar da iyalansu abinda ya faru.

Da aka tuntuɓe shi ranar Alhamis, kakakin yan sandan Abiya, Geoffrey Ogbonna, yace tuni jami'ai suka fara bincike kan lamarin. Yace za'a yi gwaji kan gawarwakin.

Mutuwa Rigar Kowa: Mutane Sama da 12 Sun Kone Kurmus a Jihar Kano

A wani labarin Wasu Motoci biyu sun yi taho mu gama a kan babban Titin Gaya-Wudil a Kano, Fasinjoji 13 sun mutu nan take

Kwamandan hukumar kiyaye haɗurra na jihar yace wasu shida sun jikkata amma ance wata Fasinja mace tace ga garinku nan a Asibitin Malam Aminu.

Yace gudun wuce ƙima da kuma kokarin tserewa juna ke haddasa Hatsari, ya yi kira ga direbobi su yi taka tsantsan a kan manyan Tituna.

Kara karanta wannan

Sabbin Rigingimu Sun Kara Ɓarkewa a Jam'iyyar PDP Kan Kuɗin Yakin Neman Zaben Atiku 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel