2023: Abinda Kauran Bauchi Ya Fada Wa Gwamna Ortom Kan Kalamansa Na Fulani, Atiku

2023: Abinda Kauran Bauchi Ya Fada Wa Gwamna Ortom Kan Kalamansa Na Fulani, Atiku

  • Gwamnann Bauchi, Bala Muhammed, ya ja hankalin takwaransa na jihar Benuwai kan kalaman da ya yi game da Fulani
  • Yayin ziyarar da suka kai masa gida, Muhammed ya gamsar da Ortom illar kalaman kuma ya nemi a janyesu
  • Bayan ganawarsu ta sirri, Ortom ya nemi afuwar yan Najeriya inda a cewarsa ba'a fahimce shi ba

Bauchi - Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya nuna takaicinsa game da kalaman takwaransa na jihar Benuwai, Samuel Ortom, cewa ba zai taɓa zaɓen Atiku Abubakar ko wani Bafullatani ba.

Premium Times ta tattaro cewa Muhammed, wanda ya karɓi baƙuncin Ortom da sauran gwamnonin G5, yace ranshi ya ɓaci saboda kalaman na ƙabilanci ne.

Gwamna Ortom ya sha alwashin ba zai taba goyon bayan ɗan takarar shugaban kasa a PDP ba da duk wani ɗan Fulani a wani Bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan

2023: Kwankwaso Ya Faɗi Sunayen Mutum Biyu Da Yake So Su Zama Shugaban Kasa

Wike, Ortom da Kauran Bauchi.
2023: Abinda Kauran Bauchi Ya Fada Wa Gwamna Ortom Kan Kalamansa Na Fulani, Atiku Hoto: Premiumtimesng
Asali: UGC

Tawagar gwamnonin G5 sun ware kansu suna yaƙar tsagin Atiku tun bayan nasarar da ya samu kan Wike a zaɓen fidda gwanin PDP a watan Mayu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Abinda gwamnan Bauchi ya gaya wa Ortom

Amma wata majiya da ta nemi a ɓoye bayananta saboda bata da hurumin magana da 'yan jarida tace, Ƙauran Bauchi ya bukaci Ortom ya gaggauta janye kalamansa.

Haka zalika Muhammed ya shawarci mambobin tawagar G5 da su guji maida fafutukar da suke ta zama tamkar ƙin jinin Musulmi.

Majiyar tace gwamna Muhammed ya yi kokarin fahimtar da takwaransa na jihar Benuwai illar da makamantan irin waɗannan kalaman ke da shi a siyasar ƙasa.

Majiyar tace:

"(Gwamna Muhammed) yace tun da baki ɗayansu da suke takun saƙa da Atiku Abubakar mabiya Addinin Kirista ne, mutane ka iya fara tunanin cewa suna faɗa da Atiku saboda Musulmi ne kuma su Kiristoci ne."

Kara karanta wannan

"Kamata Ya Yi Ace Muna Tare": Abinda Gwamnan Bauchi Ya Faɗa Wa Wike da 'Yan G5

"Ya gaya musu cewa lokacin da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya sami matsala da wasu mambobin jam'iyya, batun ya shafi kowane ɓangare, Musumai da Kiristoci, kudu da arewa."

Gwamna Ortom ya nemi afuwa bayan haka

Da yake jawabi ga manema labarai bayan taron, ɗaya daga cikin 'yan jarida ya tambayi Ortom ko yana nan kan bakarsa game da Fulani

The Cable tace Gwamna Ortom ya amsa da cewa an masa kuskuren fahimta ne, yace:

"Na gode da wannan tambaya amma zan so karin haske cewa ba haka nake nufi ba gashi an fahimce ni ta nan, ina rokon duk wanda bai ji daɗin kalamaina ba ya sani ba haka nake nufi ba, kuma ina mai neman afuwa."

A wani labarin kuma kakakin kwamitin Kamfen PDP ya yi ikirarin cewa na gaba wasu gwamnonin G5 zasu dawo rakiyar Wike, su haɗa kai da Atiku

A cikin shirin Politics Today na Channels tv, Sanata Dino Melaye, yace tun a taron kaddamar da kamfen PDP na Benuwai, ɗaya daga cikin gwamnonin ya nuan alamu.

Kara karanta wannan

Ku yi hakuri: Gwamnan da ya muzanta Fulani ya kira su 'yan ta'adda ya nemi gafararsu

Yace duk wannan rigimar da suke yi kan shugaban PDP, Iyorchia Ayu, su da kansu suka ɗakko shi suka tsaya masa har ya zama shugaban jam'iyya na ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel