Ina Kashe A Kalla miliyan N2 Duk Kwanan Duniya, Jarumar Wasan Barkwanci

Ina Kashe A Kalla miliyan N2 Duk Kwanan Duniya, Jarumar Wasan Barkwanci

  • Jarumar wasan barkwanci Ashmusy ta koka kan yawan kudaden da take kashewa a duk kwanan duniya
  • A wannan yanayi na tsadar rayuwa da tabarbarewar tattalin arziki a kasar, Ashmusy ta yi ikirarin cewa bata kashe abun da yayi kasa miliyan N2 a kullun
  • Wannan ikirari na jarumar ya haddasa cece-kuce daga jama’a inda wasu ke mamakin har nawa ta tara

Shahararriyar mai wasan barkwanci Ashmusy ta haddasa cece-kuce a shafukan soshiyal midiya bayan ta yi ikirarin cewa tana kashe a kalla naira miliyan 2 a kulla yaumin.

Ashmusy ta kara da cewar bata san yadda aka yi take kashe kudaden ba inda ta tambayi jama’a ko suma suna fuskantar irin haka.

Ashmusy
Ina Kashe A Kalla miliyan N2 Duk Kwanan Duniya, Jarumar Wasan Barkwanci Hoto: @ashmusy
Asali: Instagram

Ta rubuta a shafinta na Instagram:

“Dan Allah wai shin ni kadai ce nake kashe a kalla 2m kan matsalolin rayuwata a kullun? Ina nufin a kullun..Shin ni kadai ce> Ban san daga ina wadannan kashe kudaden suke zuwa ba amma tabbass suna zuwa. Suna billowa ne kamar daga sama.. kamar wasa! Sun bayyana.. biya 400k na abu kaza.. 700k na kaza da sauransu kamar?? A kullun.”

Kara karanta wannan

Sauya Fasalin Naira: Cikin Makonni 2 Da Sanarwa, Jama'a Sun Kai Kudi N52bn Bankuna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalli wallafarta a kasa:

Jama’a sun yi martani

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama’a a kasa:

kehrian_bernice:

“Nawa ne kudin da kika tara gaba daya?”

everything_by_katrina:

“Ba ke kadai bace f anima abun ya ishe ni, da safen nan kawai kakata ta kirani daga kauye cewa sandar dogarawarta na bukatar fenti sai da na tura 500k nan take na gaji a lalace zan kashe 5.7m a yau ina ganin, sannu yarinya.”

seyi___funmi:

"Lmao tana nufin a rana wasu lokutan kodai kece ke ciyar da dukkanin daliban makarantar firamare da ke karamar hukumar ki ne? koda baba ne yace dole sai kin kashe 2m a kullun.”

mayana.wells:

“Kenan kina kashe 30m duk wata.”

Yar Najeriya ta hadu da sharrin kawa, ta amarce da saurayinta

A wani labarin kuma, wata matashiyar budurwa ta yi tattaki tun daga kasar Dubai don halartan baikon aminiyarta kawai sai ta ga ashe ma saurayinta ne angon.

Kara karanta wannan

Ina Addu’a Kada Allah ya Bani Haihuwa, Yara Dawainiya ne: Budurwa a Bidiyo

Tun farko dai kawar ta so yiwa aminiyar tata zuwa bazata ne a wannan rana mai dumbin tarihi a rayuwarta amma sai ta tarar da babban abun al'ajabin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel