Zunzurutun Kudi Wuri na Guga Wuri Naira Biliyan 52 aka sa a Bankunan Nigeria A Satin Biyun Da Suka Gabata

Zunzurutun Kudi Wuri na Guga Wuri Naira Biliyan 52 aka sa a Bankunan Nigeria A Satin Biyun Da Suka Gabata

  • Tun bayan sanarwar Babban Bankin Nigeria kan sauya fasalin kudin kasar, yan Kasa ke tofa Albarkacin Bakin su akai.
  • Dala tayi tashin gauron zabi a kasuwar bayan fage inda yanzu dala ake canja ta akan Naira 800 duk daya.
  • A kwanan nan ma dai Hukumar hana cin Hancin da rashawa rashen jihar kano tayi dirar mikiya a kasuwar Canji kudi ta wafa

Tun bayan da babban bankin kasa ya ayyana aniyarsa ta sakewa kudin Nigeria fasali aka samu tunbidin kudi muraran wanda adadin su ya kai naira biliyan 52 a bankunan Kasar.

Akwai alamun da suke cewa adadin kudin kan karu a sati mai zuwa sabida yadda ake tunanin ko yamididin akwai kusan naira Tiriliyan uku a hannun mutane kamar yadda Jaridar The Nation ta rawaito.

Kara karanta wannan

Za mu zama marasa amfani idan muka bari Tinubu yaci zabe, Kiristocin Arewa

Babban bankin kasa yana zargin wasu yan siysa, da yan kasuwar canji da wasu yan kasuwa har ma da dillai kan sune a gaba-gaba wajen sanya kudin a bankunan.

Gwamnan Baban Banki 
Hoto: Premium Times
Zunzurutun Kudi Wuri na Guga Wuri Naira Biliyan 52 aka sa a Bankunan Nigeria A Satin Biyun Da Suka Gabata
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar The Nation din kuma tace an lura da yadda hukumomin Hana ta'annati da dukuyar kasa da sauran takwarorin ta ke umarta bankunan kan su ringa daukar bayanan iri-iren wadannan mutanen masu sanya kudin.

Akwai tsoron cewa yanayin sauya fasalin kudin zai iya shafar hada-hadar kudade, musamman ma a zaben shekarar 2023 a wajen yakukan neman zabe.

Wata majiya mai karfi da ta shedawa jaridar The Nation tace hukumomin tsaron kasar da na sirrin sun tabbatar da yadda ake wadaka da kudaden wajen sanya su a bankuna wanda suke hasashen sun kai kusan naira biliyan 52.

Kara karanta wannan

Buhari Na Shirin Kashe Biliyan 2 Domin Sabunta Motocin Aso Villa

Majiyar ta kara da cewa an umarci ko wanne banki samar da bayanan duk wanda aka ga sunzo sa irin wadan nan kudaden.

An umarci Bankunan Daukan Bayanan Masu sanya Kudade

An jiyo hukumomin jami'an tsaro na umartar dukkan nin bankunan kasar nan daukan bayan wanda suke huldar dasu musamman wanda suka zo sanya makudan kudade.

Da wannan umarnin zamu samu hanya mafi sauki da zamu samu wanda suke da niyya ko kuma suke taimakawa wajen nukusa tattalin arzikin kasar nan.

yayin da yake amsawa manema labarai tambaya, Majiyar tace

Wasu yan siyasa da wasu da ake zargin yan barandarsu ne, sun kasance a komar hukumar, baya ga yadda take sa ido a kansu kan wannan badakalar.
Wasu Gwamnonin jihohi baza su iyan biyan albashi sabida yadda cin hanci yai katutu a jihohin su, dole babban bankin kasar ya fitar da wannan tsarin.

Kara karanta wannan

An Ci Karo da Matsaloli, Gwamnatin Buhari Za ta Iya Shirya Sabon Kundin Kasafin kudi

Baya ga sauyawa kudaden Kasar fasali, baban bankin kasa na bin kudirin gwamnatin Buhari wajen yakar cin hanci da rashawa.

A ranar 26 ga watan oktoban wanna shekarar ne dai babban banki ya sanar da sauya fasalin kudin Nigeria.

Babban bankin dai na cewa "a iya watan satumba Naira Biliyan 2.73 ke yawo a tsakanin bankunan kasar mamakon naira Biliyan 3.23 da ya kamata ace ya zagaya, amma jama'a sun rike su".

Asali: Legit.ng

Online view pixel