Da dumi-duminsa: Wani abin fashewa ya tashi da daliban makaranta a jihar Kano

Da dumi-duminsa: Wani abin fashewa ya tashi da daliban makaranta a jihar Kano

Labarin dake shigo mana da duminsa na nuna cewa wani abin fashewa ya tashi a jihar Kano, Arewa maso yammacin Najeriya.

Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa ya tashi a Aba Road da ke Unguwar Sabon Gari a birnin Kanon.

Shugaban Kasuwar Sabon Gari Nafi'u Nuhu Indabo ya tabbatar da cewa lamarin ya rutsa da mutane da dama ciki har da yara ƴan makaranta.

Hotunan da aka gani a wajen ya nuna cewa da yiwuwan an yi rashin rayuka da dama kuma an ga gawar akalla mutum daya, riwayar ChannelsTV.

Jama'ar unguwa sun taru wajen yayinda wasu ke kokarin ceton wadanda suka jikkata.

Hotunan sun nuna yadda ake fito da daliban makaranta dake cikin gidan da Bam din ya tashi.

Kwamishinan ƴan sanda na Kano ya ce abin da ya fashe a yau gas ne ba bam ba. Amma suna gudanar da karin bincike.

Kara karanta wannan

Matasa sun nuna fushinsu yayin da wata Naomi Goni ta kara ɓatanci ga Annabi SAW, an kama 3

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutum hudu sun rasa ransu.

Da dumi-duminsa: Wani Bam ya tashi a daliban makaranta a jihar Kano
Da dumi-duminsa: Wani Bam ya tashi a daliban makaranta a jihar Kano
Asali: Original

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel