Abba Gida-Gida Zai Lashe Zaben Gwamnan Jihar Kano, Binciken Anap Foundation

Abba Gida-Gida Zai Lashe Zaben Gwamnan Jihar Kano, Binciken Anap Foundation

  • Gidauniyar Anap Foundation ta gudanar da kuri'ar jin ra'ayi kan wanda zai lashe zaben gwamna a jihar Kano
  • Yanzu saura kimanin watanni biyar a gudanar da zaben gwamnoni a Najeriya kamar yadda INEC ta tsara
  • Akwai manyan yan takara hudu da zasu yi musharaka a zaben gwamnan jihar Kano

Yayinda zabukan shugaban kasa da gwamnoni ke gabatowa, gidauniyar Anap karkashin jagorancin Mamallalin bankin StanbicIBTC ta gudanar da binciken jin ra'ayi a jihohin Najeriya.

BInciken da Anap Foundation ya gudanar a jihar Kano ya nuna cewa Abba Kabir-Yusuf na jam'iyyar New Nigeria People Party (NNPP) ne ke kan gaba wajen yiwuwan nasara.

Zaben jin ra'ayin da NOIPolls ta gudanar a Oktoba ya nuna cewa Abba Gida-Gida na NNPP da Nasiru Gawuna na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ne zasu fafata.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC: Kotu za ta tabbatar ban fadi zabe ba, za a dawo min da kujera ta

Zaben Kano
Abba Gida-Gida Zai Lashe Zaben Gwamnan Jihar Kano, Binciken Anap Foundation Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar rahoton binciken:

"Sakamakon ya nuna cewa Abba Kabir Yusuf na kan gaba saboda kashi 29% na mutane sun ce shi zasu kadawa kuri'a idan akayi zabe yau; yayinda kashi 21% suka ce Nasiru Yusuf Gawuna na APC zasu kadawa."
"Mohammed Sadiq Wali na PDP kuwa shi zai so na uku inda kashi 3% kacal suka ce zasu zabeshi."
"Amma kuri'ar jin ra'ayin ya nun acewa kashi 30% sun ki bayyana wannan zasu kadawa kuri'a yayinda kashi 11% sukace har yanzu basu san wanda zasu kadawa ba."

Masu binciken sun bayyana cewa kuri'ar jin ra'ayin da suka gudana na nuni ga cewa da yiwuwan mutanen da fita kada kur'a a zaben 2023 za su fi na 2019 yawa.

Su wanene yan takaran gwamna a Kano

Rahoton Anap Foundation ya nuna cewa akwai yan takara hudu wadanda ake ganin mutum daya cikinsu ne zai samu nasara a zaben da zai gudana a Maris 2023.

Kara karanta wannan

Sai Ta An yi Addu'a, Ubangiji Bai Fada Min Za'a Yi Zabe A 2023 Ba, Fasto Enoch Adeboye

Sun hada da:

1. Dr Nasiru Yusufu Gawuna na jam'iyyar APC

2. Injiniya Kabir Abba Yusuf na jam'iyyar NNPP

3. Hanarabul Mohammed Sadiq Wali na jam'iyyar PDP

4. Hanarabul Sha'aban Ibrahim Sharada na jam'iyyar ADP

Abba Kabir Yusuf dai ya yi takara a zaben 2019 inda ya zo na biyu karkashin jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel