Babu 'Yan Adawan Tinubu a Zamfara, a Tafi Wata Jihar a Nemi Kuri’u Inji Shugaban Kamfe

Babu 'Yan Adawan Tinubu a Zamfara, a Tafi Wata Jihar a Nemi Kuri’u Inji Shugaban Kamfe

  • Kabiru Garba Marafa ya yi wa Bola Ahmed Tinubu albishir tun yanzu cewa ya ci zabe a jihar Zamfara
  • Shugaban kwamitin kamfe na jihar yace babu wani wanda zai iya yi wa jam’iyyar APC adawa a Zamfara
  • Sanata Kabiru Garba Marafa ya na so Dauda Lawal mai takarar Gwamna a PDP, ya dawo APC mai mulki

Zamfara - Shugaban yakin neman zaben Bola Ahmed Tinubu a jihar Zamfara, Kabiru Garba Marafa yana ganin jam’iyyar APC mai mulki ta ci zabe ta gama.

A rahoton da Daily Trust ta fitar a ranar Litinin, 7 ga watan Nuwamba 2022, an ji Sanata Kabiru Garba Marafa ya ba APC nasara a zaben shugaban kasa.

Kabiru Garba Marafa ya fadawa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu cewa ya karkatar da neman zabensa zuwa wasu jihohi, domin babu ‘yan adawa a Zamfara.

Kara karanta wannan

Dattawan Yarbawa Sun Tsaida 'Dan Takaransu Tsakanin Tinubu, Atiku, Obi da Kwankwaso

Shugaban kwamitin zaben ya bayyana haka wajen kaddamar da yakin takarar Tinubu/Shettima.

Tsohon Sanatan na APC yace mutanen jihar Zamfara za su fito kwansu da kwarkwata domin zabar Bola Tinubu a ranar 25 ga watan Fubrairun 2023.

Matawalle ya rabu da Zamfara - Marafa

Haka zalika Marafa ya yi kira ga Bello Matawalle wanda shi ne shugaban kamfe na jihohin Arewa maso yamma, da ya maida hankalinsa a kan wasu jihohi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bola Tinubu
Bola Tinubu da manyan APC a Ekiti Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

This Day ta rahoto ‘dan siyasar yana ba Gwamnansa shawara ya sa karfinsa a Kano, Kaduna, Kebbi, Sokoto, da Jigawa domin tuni APC ta karbe jihar Zamfara.

“Babu hamayya a jihar Zamfara. Za ku iya fada ne babu Sarkin yaki? A'a! ‘Yan adawa a Zamfara ba su da jagora. Saboda haka, an ci yakin Zamfara.”

- Kabiru Garba Marafa

Kara karanta wannan

Ana Zargin Gwamnan PDP da Ya Raba Jiha da Atiku Zai Yi wa Tinubu Aiki a Zaben 2023

Kyau Dauda Lawal ya dawo gida

Marafa wanda ya wakilci Zamfara ta tsakiya a majalisar dattawa, ya roki Gwamna Matawalle ya kyale ‘Dan takaran PDP, Dauda Lawal ya dawo APC.

‘Dan siyasar yace za su ba Lawal makonni biyu zuwa uku ya nemi gafara domin a yafe masa, sai a hada-kai domin ayi wa jam’iyyar APC aiki a tare.

Jigon yake cewa mukamin gwamna kamar kujerar wanzami ce, sai wani ya tashi sannan za a iya yi wa wani aski, yace yanzu akwai wani a kujerar.

Rashin tsaro a Zamfara

Dazu aka fahimci cewa duk da nasarorin da ake sam a bangaren tsaro, har yanzu ana fama da matsalar kashe-kashe da garkuwa da mutane a Zamfara.

Baya ga Mai martaba, Mai garin Kwangami, Muhammad Galadima da ya shiga hannu, an bar mutanen kauen da-dama da rauni bayan an kai hari.

Kara karanta wannan

2023: APC ta Tarbi Fiye Da Mutum 1000 Da Suka Sauya Sheka Daga PDP A Zamfara

Asali: Legit.ng

Online view pixel