Tsohon ‘Dan Majalisar Jihar Kaduna, Alhaji Danlami, Ya Kwanta Dama

Tsohon ‘Dan Majalisar Jihar Kaduna, Alhaji Danlami, Ya Kwanta Dama

  • Alhaji Danlami Dan Inna Likoro, tsohon ‘dan majalisar jihar Kaduna da ya wakilci mazabar Kudan ya kwanta dama
  • Dan Inna ya rasu a yammacin Lahadi bayan yayi fama da gajeriyar rashin lafiya bayan gwagwarmaya da yayi yana raba Zakka
  • ‘Dan Takarar Gwamnan Kaduna a PDP, Ashiru Isah Kudan ya kwatanta rasuwarsa da babban rashi a lokacin da jam’iyyar ke matukar bukatarsa da gogewarsa

Kaduna - Tsohon ‘dan majalisa da ya wakilci mazabar Kudan a majalisar jihar Kaduna tsakanin 2011 zuwa 2019, Alhaji Danlami Dan Inna Likoro, ya kwanta dama.

Danlami Dan InnaLikoro
Tsohon ‘Dan Majalisar Jihar Kaduna, Alhaji Danlami, Ya Kwanta Dama. Hoto daga dailytrust.con
Asali: UGC

A yayin tabbatar da faruwar lamarin, iyalan tsohon ‘dan majalisar sun ce ya rasu da yammacin Lahadi sakamakon gajeriyar rashin lafiya kuma ya dinga aikin bayar da Zakkah kafin lokacin, jaridar Daily Trust ta rahoto .

Kara karanta wannan

Shugaban Masu Rinjaye A Majalisar Wakilai Doguwa Ya Magantu Game Da Batun Sauya Shekarsa Daga APC

Har zuwa rasuwarsa, Likoro shi ne ‘dan takarar kujerar da ya bari na yankinsa a karkashin jam’iyyar PDP.

‘Dan Takarar Gwamna Yayi Ta’aziyya

A sakon ta’aziyya ta bakin hadiminsa na fannin yada labarai, Shuaibu Gimi, ‘dan takarar kujerar gwamnan jihar Kaduna a jam’iyyar PDP, Alhaji Isah Ashiru Kudan, ya kwatanta tsohon ‘dan majalisar da gogaggen ‘dan siyasa da ya bayar da gudumawa wurin ganin cigaban jam’iyyar da jihar Kaduna.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ashiru ya bayyana cewa, marigayin ya mayar da hankali wurin ganin cigaban jam’iyyar kuma yana da rikakkun ra’ayin damokaradiyya wanda ya rasu yayin da jam’iyya ke matukar bukatar gudumawarsa da gogewarsa.

Daily Trust ta rahoto cewa, ya jajantawa iyalansa da dukkan iyalan PDP na kasarNajeriya ballantana reshen jihar Kaduna.

Allah Yayi wa Jigon APC kuma 'Dan Takarar Kujerar Sanata, Rasuwa

A wani labari na daban, jigon jam'iyyar APC a jihar Jigawa kuma 'dan takarar kujerar sanatan Jigawa ta tsakiya, Alhaji Tijjani Ibrahim Gaya, ya kwanta dama.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Tabbatar Da Uba Sani A Matsayin Sahihin Dan Takaran Gwamnan APC a Kaduna

Fitaccen 'dan siyasan ya rasu ne sakamakon gajeriyar rashin lafiya da yayi fama da ita kamar yadda takardar da gwamnan Jigawa ya fitar ta hannun kwamishinan ayyuka na musamman ta bayyana.

Zabbaben gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya aike da sakon ta'ziyyarsa ga iyalansa da jama'ar Jigawa kan rasuwar 'dan takarar.

Gwamnan ya kwatanta Ibrahim Gaya a matsayin mutumin kirki, jajirtaccen shugaba kuma madubin dubawa ga matasa, wanda ya sadaukar da dukkan rasyuwarsa wurin bautawa jama'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel