Da duminsa: Allah Yayi wa Jigon APC kuma 'Dan Takarar Kujerar Sanata, Rasuwa
- Allah ya yi wa Alhaji Tijjani Ibrahim Gaya, fitaccen jigon APC kuma 'dan takarar kujerar sanata na Jigawa ta tsakiya, rasuwa
- Kamar yadda takardar ta'aziyyar da Gwamna Badaru ya fitar ta bayyana, ya rasu sakamakon gajeriyar rashin lafiya da yayi fama da ita
- Kafin rasuwarsa, mutum ne mai jajircewa da shugabanci nagari kuma madubin dubawar matasa, kamar yadda Gwamnan Jigawa ya sanar
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jigawa - Jigon jam'iyyar APC a jihar Jigawa kuma 'dan takarar kujerar sanatan Jigawa ta tsakiya, Alhaji Tijjani Ibrahim Gaya, ya kwanta dama.
Fitaccen 'dan siyasan ya rasu ne sakamakon gajeriyar rashin lafiya da yayi fama da ita kamar yadda takardar da gwamnan Jigawa ya fitar ta hannun kwamishinan ayyuka na musamman ta bayyana.
Zabbaben gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya aike da sakon ta'ziyyarsa ga iyalansa da jama'ar Jigawa kan rasuwar 'dan takarar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Gwamnan ya kwatanta Ibrahim Gaya a matsayin mutumin kirki, jajirtaccen shugaba kuma madubin dubawa ga matasa, wanda ya sadaukar da dukkan rasyuwarsa wurin bautawa jama'a.
"Rasuwar Tijjani Ibrahim Gaya ta zo da matukar bada mamaki gareni da jama'ar Jigawa. Kowanne rai zai dandana mutuwa. Fatanmu shine mu samu kyakyawan karshe kuma babu shakka 'dan uwanmu ya samu kyakyawan karshe bayan fama da gajeriyar rashin lafiya," Gwamnan yace.
Gwamnan yayi addu'a kan Allah Subhanahu wata'ala ya sanya shi a Al jannar Firdausi kuma ya bai wa iyalansa hakurin jure rashin.
'Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar babban jigon APC ɗan takara a 2023
A wani labari na daban, 'yan bindigan sun sace mahaifiyar ɗan takarar kujerar Sanata na shiyyar jihar Jigawa ta tsakiya, Honorabul Tijjani Ibrahim Gaya.
Leadership ta ruwaito cewa matar ƴar kimanin shekara 70 a duniya, Hajiya Jaja, ta shiga hannun masu garkuwa da mutanen ne a gidanta da ke ƙaramar hukumar Kiyawa, jihar Jigawa.
Mai magana da yawun hukumar yan sanda reshen jihar dake arewa maso yammacin Najeriya, DSP Lawal Shisu, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Kakakin yan sandan ya bayyana cewa maharan sun sace mahaifiyar ɗan takarar ne a farkon awannin ranar Talata, 21 ga watan Yuni, 2022, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Asali: Legit.ng