Buhari Ya Amince da Fitar da Ton 12,000 Na Hatsi a Ba Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa

Buhari Ya Amince da Fitar da Ton 12,000 Na Hatsi a Ba Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya waiwayi wadanda ambaliyar ruwa ta taba a shekarar nan a fadin Najeriya
  • Rahotanni sun bayyana yadda kasar nan ke cikin tashin hankali yayin da ambaliyar ruwa ta lalata gidaje da dukiyoyi

Za a samar da kayan abinci da ya kai ton 12,000 ga mutanen da abin ya shafa daga ofishin shugaban kasa

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a cire ton 12,000 na hatsi a raba wa mutanen da ambaliyar ruwa ta rutsa dasu a fadin kasar nan.

Sadiya Umar Faruk, ministar jin kai ta Najeriya ne ta bayyana hakan a ranar Alhamis a taron ministoci da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja.

Buhari zai ba da tallafi ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa
Buhari Ya Amince da Fitar da Ton 12,000 Na Hatsi a Ba Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A cewar ministar, ya zuwa yanzu, gwamnatin Buhari ta ba da tallafi da kuma kai dauki ga jihohi 28 a fadin kasar nan kan wannan ambaliya, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan Ta’adda Sun Dasa Bam Ta Karkashin Kasa a Kaduna, Mutum 2 Sun Halaka

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarta:

“Ma’aikatar, ta hannun hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), ta ba da kayan tallafin gaggawa, ciki har da kayan tafi da gidanka na tsaftace ruwa, jiragen ruwan nema da ceto, da kuma kayayyakin ceto da ujila don tabbatar da kubutar da rayuka da ba da tallafi ga gajiyayyu da dama.
“Ya zuwa yanzu, NEMA ta iya kai wa ga mutane 1,427,370 da suka rabu da gidajensu a jihohi 28 da babban birnin tarayya (FCT).”

Hakazalika, ta ce tuni aka fara raba kayan abinci, magani da kayan gini ga wadanda wannan iftila’i ya shafa a fadin kasar.

Jihohin da suka saura da kuma halin da ake ciki

Ta bayyana cewa, jihohin da suka saura sun hada da Akwa Ibom, Kuros Riba, Kwara, Zamfara, Katsina, Kebbi, Borno da Gombe, Ripples Nigeria ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Magidanci ya gamu da fushin alkali yayin da ya daba wa surukinsa kwalba a kai

Baya ga ba da umarnin da Buhari ya yi na ba da hatsi, ta kuma yi karin haske da cewa, kwamitin shugaban kasa kan ambaliyar ruwa karkashin jagorancin Aliko Dangote ya samar da kayan abinci da darajarsa ta kai N1.5bn.

Hakazalika, tuni aka far aba mutanen da lamarin ya shafa kyautar tantuna domin zaman wucin gadi a jihohi 22 a Najeriya.

‘Yan Najeriya suna ci gaba da fuskantar tasirin ambaliyar ruwa a jihohi daban-daban na kasar.

Jerin sunayen jihohi 32 na Najeriya da za a fuskanci ambaliyar ruwa a 2022

A bangare guda, darakta janar na Nigeria Hydrological Services Agency, NIHSA, Clement Nze, ya ce bayanai daga binciken ambaliyar ruwa na shekarar 2022 sun nuna cewa za a samu ambaliyar ruwa a jihohi 32 na kasar nan har da babban birnin tarayya na Abuja.

A yayin jawabi a Abuja lokacin gabatar da kiyasin hukumar na wuraren da za a iya samun ambaliyar ruwa, ya bayyana jihohin Adamawa, Abia, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Cross-River, Delta, Ebonyi, Ekiti, Edo a cikin wuraren da ake kyautata tsammanin samun ambaliyar ruwan.

Kara karanta wannan

Ministan farko na sufurin jiragen sama a Najeriya, babban mai kare Nnamdi Kanu ya rasu

Asali: Legit.ng

Online view pixel