Jerin sunayen jihohi 32 na Najeriya da za a fuskanci ambaliyar ruwa a 2022

Jerin sunayen jihohi 32 na Najeriya da za a fuskanci ambaliyar ruwa a 2022

  • Hukumar NIHSA ta bayyana cewa, za a samu ambaliyar ruwa a kanan hukumomi 233 na jihohi 32 a fadin kasar nan har da FCT
  • Daga cikin jihohin da shugaban hukumar ya ambata akwai Adamawa, Abia, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Cross-River, Delta
  • Ya yi kira ga masu shiri, masu ruwa da tsaki da jama'ar gari da a dauka matakin karanta ambaliyar don takaita asarar rayuka da kadarori

FCT, Abuja - Darakta janar na Nigeria Hydrological Services Agency, NIHSA, Clement Nze, ya ce bayanai daga binciken ambaliyar ruwa na shekarar 2022 sun nuna cewa za a samu ambaliyar ruwa a jihohi 32 na kasar nan har da babban birnin tarayya na Abuja.

A yayin jawabi a Abuja lokacin gabatar da kiyasin hukumar na wuraren da za a iya samun ambaliyar ruwa, ya bayyana jihohin Adamawa, Abia, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Cross-River, Delta, Ebonyi, Ekiti, Edo a cikin wuraren da ake kyautata tsammanin samun ambaliyar ruwan.

Kara karanta wannan

Kano: Ƴan Sanda Sun Kama Mota Maƙare Da Kayan Haɗa Bamai-Bamai Da Bindigu

Jerin sunayen jihohi 32 na Najeriya da za a fusknaci ambaliyar ruwa a 2022
Jerin sunayen jihohi 32 na Najeriya da za a fusknaci ambaliyar ruwa a 2022. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

Har ila yau, sauran jihohin da ake kyautata zaton samun ambaliyar ruwan sun hada da Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Kebbi, Kogi, Kwara, Legas, Nasarawa, Niger, Ogun, Ondo, Oyo, Rivers, Sokoto, Taraba, Zamfara da FCT Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce kananan hukumomin 212 a jihohi 35 na kasar nan har da FCT sun hada da inda ake zaton samun matsakaicin ambaliyar ruwa.

NIHSA ta bayyana a shafinta cewa, sauran kananan hukumomin 329 sun hada da inda akwai yuwuwar samun ambaliyar ruwa.

Nze ya jaddada cewa, a bangaren tsanantar ambaliyar ruwan, wuararen da ake kyautata zaton suna sassan kananan hukumomi 57 a kasar nan kuma a watannin Afirilu, Mayu da Yuni za a yi hakan yayin da sauran kananan hukumomi 220 ana tsammanin samun ambaliyar ruwan ne a watan Yuni, Augusta da Satumba.

Ya ce kananan hukumomi 38 sun fada a watannin Oktoba ne da Nuwamban shekarar nan.

Kara karanta wannan

Kotu ta yankewa Bature hukuncin kisa kan laifin kashe matarsa Zainab da 'yarsa a Legas

Ya ce ambaliyar ruwa a watannin nan da aka ambato yana da matukar tasiri kan yawan jama'a, noma, kiwon dabbobi, ababen more rayuwa da muhalli.

"Jihohin Ribas, Bayelsa, Cross River, Delta, Edo, Legas, Ogun da Ondo ana tsammanin za su samu ambaliyar ruwan ne sakamakon karin yawan ruwa sama da matakin teku wanda zai yi tasiri a kan kamun kifi da dabbobin da ke cikin ruwa," yace.

Nze ya jaddada cewa duk wasu masu shiri, masu tsari da yanke hukunci, manoma, masu ruwa da tsaki da jama'ar gari su fara daukan matakan kiyayewa domin Inganta muhalli da yawan barnar da za a samu na rayuka da kadarori.

A bangarensa, Darakta Janar na NEMA, Alhaji Mustapha Habib Ahmed, ya ce ya zama dole ga jama'a da gwamnati da su dauka alhakin bada gudumawa wurin kiyaye ibtila'in a maimakon barin dukkan nauyin a kan gwamnatin tarayya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel