Yan Ta’adda Sun Dasa Bam Ta Karkashin Kasa a Kaduna, Mutum 2 Sun Halaka

Yan Ta’adda Sun Dasa Bam Ta Karkashin Kasa a Kaduna, Mutum 2 Sun Halaka

  • Mutane biyu sun halaka bayan wani abun fashewa da aka binne ta karkashin kasa ya tashi da su
  • Lamarin ya afku ne a Zangon Tofa, yankin Kabrasha da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna
  • Motar mutanen ya bi ta kan bam din wanda ake zaton yan ta'addan ne suka binne shi a karkashin kasa, sai kuma ya tashi da su

Kaduna - Wasu mazauna Kaduna biyu sun rasa rayukansu sakamakon tashin bam da aka dasa ta karkashin kasa a karamar hukumar Chikun da ke jihar.

Lamarin ya afku ne da misalin karfe 2:00 na ranar Alhamis, 3 ga watan Nuwamba bayan motar mutanen ya bi ta kan bam din da ake zargin yan ta’adda ne suka binne shi a wani wuri da ake kira Zangon Tofa a yankina Kabrasha.

Kara karanta wannan

Magidanci ya gamu da fushin alkali yayin da ya daba wa surukinsa kwalba a kai

Jihar Kaduna
Yan Ta’adda Sun Dasa Bam Ta Karkashin Kasa a Kaduna, Mutum 2 Sun Halaka Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa mazauna kauyen na jigilar amfanin gona da aka girbe ne lokacin da lamarin ya afku.

Da yake tabbatar da lamarin, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya bayyana sunayen mutanen da suka rasu a matsayin Babajo Alhaji Tanimu da Safiyanu Ibrahim.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa, gwamnatin jihar na jiran karin bayani.

Ya kuma ce Gwamna Nasir El-Rufai ya mika ta’aziyya ga iyalan wadanda abun ya ritsa da su.

El-Rufai wanda ya yi addu’a kan Allah ya ji kan mamatan, ya roki mazauna yankin da su kwantar da hankulansu, Channels TV ta rahoto.

'Ku Agaza Mana': Iyaye Sun Koka Yayin da Yan Bindiga Suka Sace Kananan Yara Sama da 30 a Jihar Buhari

A wani labari na daban, mun ji cewa iyaye a garuruwan karamar hukumar Faskari, inda yan bindiga suka sace yara 39 yayin da suke tsaka da aiki a gona sun roki gwamnati da ta ceto yaran daga hannun wadanda suka sace su.

Kara karanta wannan

Bayan Abuja, Jami'an EFCC Sun Kai Simame Shagunan Yan Canji a Jihar Kano

Daily Trust ta rahoto cewa yan bindigar sun mamaye wata gona a ranar Lahadi inda suka yi awon gaba da yara fiye da 40 da suka hada da maza da mata yayin da suke tsaka da aiki.

Wata majiya a garin Mairuwa, inda harin yafi muni ta ce yan bindigar sun mamaye gonar sannan suka fara harbi kan mai uwa da wahabi kafin suka sace ma'aikatan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel