'Yan Sanda Sun Tsere A Yayin Da Yan Bindiga Suka Sace Fasinjoji 9 A Babban Jihar Najeriya

'Yan Sanda Sun Tsere A Yayin Da Yan Bindiga Suka Sace Fasinjoji 9 A Babban Jihar Najeriya

  • Wasu mahara da ake zargin masu garkuwa ne sun sace fasinjoji tara a hanyar Emuoha a jihar Ribas
  • Wani mazaunin unguwar ya bada bayanin yadda wasu yan sandan suka tsere yayin da maharan ke shiga da mutane daji
  • Grace Iringe-Koko, mai magana da yawun yan sandan jihar Ribas ta ce bata riga ta samu labarin ba

Jihar Ribas - Yan bindiga sun sace fasinjoji tara a wata motar haya a hanyar Emuoha na East-West Road a jihar Ribas, The Punch ta rahoto.

Yan daba sun dade suna adabar hanyar Emuoha zuwa Kalabari suna kwace ababen hawa suna kuma sace matafiya a shekarun da suka gabata.

Yan Bindiga
'Yan Sanda Sun Gudu A Yayin Da Yan Bindiga Suka Sace Fasinjoji 9 A Ribas. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Wani mazaunin garin ya bada bayani dalla-dalla yadda abin ya faru

A mazaunin garin Odegu a karamar hukumar Emuoha, Prince Chukwu, ya shaida wa manema labarai cewa lamarin ya faru ne a iyakar Evekwu da Rumuodogo a karamar hukumar Emohua a daren ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Magidanci ya gamu da fushin alkali yayin da ya daba wa surukinsa kwalba a kai

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Chukwu ya ce yan bindigan sun tare mota bas, suka umurci dukkan fasinjojin su fito tare da direban suka tisa keyarsu cikin daji.

Ya ce kafin yan sandan da aka kira su isa wurin, yan daban sun tsere tare da wadanda suka sace.

Mr Chukwu ya koka cewa sun ficewar yan banga da ake kira OSPAC, bata gari sun dawo kan hanyar.

Ya ce:

"Daren jiya (Laraba), sun sace mutane tara a iyakar Evekwu da Rumuodogo.
"Kafin yan sandan da ke Elibrada junction su iso wurin, masu garkuwan sun shige daji tare da wadanda suka sace. Har yan sandan da ke Rumuj sun tsere.
"Abin da ya fi dacewa shine a dawo da OSPAC saboda sun san wadannan bata garin da hanyoyin da suke bi.
"Su manta da siyasa da suke yi su dawo da OSPAC. Wannan shine shawara ta."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Sojoji da 'Yan Sanda Sun Sheƙe Hatsabiban Yan Bindiga Uku, An Gano Wani Abu a Jikinsu

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar, Grace Iringe-Koko, ta ce bata riga ta samu rahoton afkuwar lamarin ba.

Ba Sojojin Amurka Ne Suka Kai Samame A Abuja Ba, In Ji Mazaunin Unguwa

Sojojin Amurka ba su cikin wadanda suka kai samame a rukunin gidaje na Trademore da ke Lugbe, babban birnin tarayya, Abuja, in ji wani mazaunin unguwar, Daily Trust ta rahoto.

Mazaunin, wanda ya tabbatar an kawo samame unguwar, ya ce kawai dan kasar waje daya aka gani cikin jami'an da suka kawo samamen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel