Babban Abin da Ya sa Muka Hakura, Muka bude Jami’o’i Bayan Wata 8 inji ASUU

Babban Abin da Ya sa Muka Hakura, Muka bude Jami’o’i Bayan Wata 8 inji ASUU

  • An tattauna da shugaban kungiyar ASUU a game da dogon yajin-aikin da malaman jami’a suka yi
  • Farfesa Emmanuel Osodeke yace hukuncin kotu ne ya yi sanadiyyar komawansu aji bayan watanni 8
  • An koma aiki ne ba tare da an cin ma matsaya ko an sa hannu a wata yarjejeniya ba inji Osodeke

Lagos - Shugaban kungiyar ASUU ta malaman jami’a, Emmanuel Osodeke yace hukuncin kotu ne babban abin da ya tursasa masu komawa bakin aiki.

The Cable ta rahoto Farfesa Emmanuel Osodeke yana mai cewa malamai sun janye yajin-aikin da su ke yi ne saboda Alkali ya umarci su bude makarantu.

Kungiyar ASUU tace duk da an janye yajin-aikin bayan watanni takwas, har yanzu ba ta cin ma matsaya da gwamnatin tarayya kan wasu batutuwan ba.

Da aka zanta da shi a gidan talabijin na Channels, Farfesan yace kungiyarsu tana sa ran gwamnati za tayi abin da ya dace tun da sun dawo bakin aikinsu.

A hirar da aka yi da shi, Osodeke yace duk da shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya sa baki a lamarin, kotu tayi tasiri wajen daukar matsaya.

Kotu muka yi wa biyayya - ASUU

"Babban dalilin dawowar mu aiki shi ne yi wa umarnin kotu biyayya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaban ASUU
Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Ba a gama shawo kan matsalolin ba, kuma babu wata yarjejeniya da aka cin ma. Saboda mun dawo aiki ne saboda mu kungiya ce mai bin doka.
Ba mu son yi wani abin da zai saba doka. Muna sa ran sa-bakin da shugaban majalisa ya yi, kamar yadda ya yi alkawari zai kawo mafita da wuri."

- Farfesa Emmanuel Osodeke

Jaridar tace da aka tambayi Osodeke ko za su koma aji, ya tabbatar da dole haka za ayi.

Emmanuel Osodeke ya bada shawara

Shugaban kungiyar ya caccaki Ministan kwadago, wanda yake zargi da kokarin tursasawa malamai koyar da dalibai, a maimakon sulhu da gwamnati.

Farfesan yake cewa duk kasar da tayi wasa da ilmi ba ta nemi zaman lafiya ba, ya yi kira ga gwamnati mai zuwa ta ware 16% ga bangaren cikin kasafin kudi.

Ma'aikatan lafiya za su daina aiki?

Kwanaki kun samu labari akwai yiwuwar kungiyar SSAUTHRIAI ta manyan malaman lafiya da Ma’aikatan cibiyoyin bincike za su daina aiki a watan nan.

Shugaban kungiyar ta kasa ya ba gwamnati mako daya ta biya su hakkokinsu. Kabir Mustapha yace suna neman ragowar wasu 40% na alawus din shiga hadari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel