Lai Mohammed Ya Koka Kan N345m da Aka Warewa Ma’aikatarsa, Yace Kan Shi Ya Daure

Lai Mohammed Ya Koka Kan N345m da Aka Warewa Ma’aikatarsa, Yace Kan Shi Ya Daure

  • Ministan yada labarai da al’adu na Najeriya, Alhaji Lai Mohammed, ya koka kan yadda aka ware N345 miliyan matsayin kasafin ma’aikatarsa a shekarar 2023
  • Mohammed yace bai ma san ta inda zai fara ba domin kan shi ya kulle, suna neman kudin bayyana nasarorin mulkin Buhari a yayin da wa’adin mulki yazo karshe
  • Ya sanar da cewa dukkan hukumomin dake karkashin ma’aikatarsa an zabtare musu kasafin kudi inda yace idan ana don aiki, a karo musu kudi

FCT, Abuja - Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, a ranar Juma’a ya koka kan N345 miliyan da aka yi kasafi domin manyan ayyuka a ma’aikatarsa a shekarar 2023 inda ya kwatanta hakan da abinda ba zai taba isarsu ba.

Lai Mohammed
Lai Mohammed Ya Koka Kan N345m da Aka Warewa Ma’aikatarsa, Yace Kan Shi Ya Daure. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ministan wanda ya bayyana hakan yayin da ya bayyana a gaban kwamitin yada labarai, wayar da kan kasa, dokoki da oda, yace ma’aikatar tana bukatar isassun kudi domin ta iya sauke Nauyin dake kanta yadda ya dace ballantana wadanda suka shafi zabe da kidayar 2023.

Kara karanta wannan

Addu'a Muke Bukata Daga Amurka Ba Wai Su Tsorata Mu Ba, Ministan Buhari

Yace ma’aikatar yada labarai tana bukatar isassun kudi domin bayyana nasarorin shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin da wa’adin mulkinsa ke gangarewa, yaki da labaran bogi, kalaman kiyayya da sauransu wadanda ke barazana ga kasantuwar Najeriya kasa guda.

“Babu lokacin da yafi dacewa ma’aikatar yada labarai ta samu kudi kamar yanzu. Ban san me zan yi da N345 miliyan ba. Ban san ta inda zan fara ba. Ban san yadda zamu tsallake ba. Idan kuna tsammanin da yawa daga gare mu, to ku bamu isassun kudi.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

- Yace.

Ya jajanta yadda manyan ayyukan ma’aikatarsa aka zabtare su daga N1 biliyan da aka bayar a 2022 zuwa N345 a 2023 wanda yace lokaci ne mafi muhimmanci ga ma’aikatar, Daily Trust ta rahoto.

Mohammed ya kara da jajanta cewa kudaden da hukumomin dake karkashin ma’aikatarsa suka yi kasafi duk an zabtare.

Kara karanta wannan

Lai Mohammed: Ina Matukar Baƙin Ciki, Kuɗaɗen Da Aka Keɓe Don Yaƙi Da Labaran Ƙarya Bai Isa Ba

Shugaban kwamitin, Odebunmi Olusegun wanda ya koka kan karancin kasafin da aka yi wa ma’aikatar, ya kara da cewa ya dace a samarwa ma’aikatar kudin da take so don tayi abinda ya dace.

Lai Mohammed: Ina Matukar Baƙin Ciki, Kuɗaɗen Da Aka Keɓe Don Yaƙi Da Labaran Ƙarya Bai Isa Ba

A wani labari na daban, ministan Watsa Labarai da Al'adu, Lai Mohammed, a ranar Talata, ya ce rashin isashen kudi da ake ware wa ma'aikatarsa duk shekara yana kawo cikas wurin yaki da labaran karya da maganganun kiyayya.

Mohammed ya bayyana hakan ne lokacin da ya gabata a gaban kwamitin majalisar tarayya ya sadarwa don kare kasafin ma'aikatansa na 2023, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel