Lai Mohammed: Ina Matukar Baƙin Ciki, Kuɗaɗen Da Aka Keɓe Don Yaƙi Da Labaran Ƙarya Bai Isa Ba

Lai Mohammed: Ina Matukar Baƙin Ciki, Kuɗaɗen Da Aka Keɓe Don Yaƙi Da Labaran Ƙarya Bai Isa Ba

  • Ministan Labarai da Al'adun Najeriya, Alhaji Lai Mohammed, ya koka kan rage wa ma'aikatarsa kudi a kasafin 2023, yana mai cewa hakan ya saka shi bakin ciki
  • Mohammed ya ce kudin da aka ware wa ma'aikatarsa baya isa su yi yaki da labaran karya da na kiyayya
  • Ministan ya yi wannan korafin ne a lokacin da ya bayyana gaban kwamitin Watsa Labarai na Majalisar Dattawa a ranar Talata

FCT Abuja - Ministan Watsa Labarai da Al'adu, Lai Mohammed, a ranar Talata, ya ce rashin isashen kudi da ake ware wa ma'aikatarsa duk shekara yana kawo cikas wurin yaki da labaran karya da maganganun kiyayya.

Mohammed ya bayyana hakan ne lokacin da ya gabata a gaban kwamitin majalisar tarayya ya sadarwa don kare kasafin ma'aikatansa na 2023, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda budurwa ta cancarawa saurayinta aski mai kyau ya girgiza intanet

Lai Mohd
Lai Mohammed: Ina Matukar Baƙin Ciki, Kuɗaɗen Da Aka Keɓe Don Yaƙi Da Labaran Ƙarya Bai Isa Ba. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Kudin da aka ware wa ma'aikatan watsa labarai ba zai isa yaki da labaran karya ba - Lai Mohammed

Ya ce ma'aikatar na bukatar isashen kudi domin yaki da labaran karya, labarai na kuskure da kalaman kiyayya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

"Idan akwai ma'aikatar da ya kamata a bata isashen kudi kuma kada a rika datse mata kudi duk shekara, ma'aikatar labarai ne.
"Gargadin harin ta'addanci da Amurka da wasu kasashe suka yi a Najeriya, duk da an karyata, ba a yi yadda ya dace ba don tabbatar da hasashen na kuskure bai zama gaskiya ba.
"Ma'aikatar ta fi gazawa wajen aiwatar da muhimman ayyukanta na wayar da kan yan Najeriya a kowane lokaci game da matsayin gwamnati kan batutuwa masu muhimmanci saboda rage kasafin kudi duk shekara."

Ban ji dadin rage mana kasafin kudi ba - Lai Mohammed

Kara karanta wannan

2023: Atiku ya yi nadi mai muhimmanci, ya ba wani dan Katsina mukamin babban sakatare

Ya cigaba da cewa:

"Ya ku sanannun sanatoci, ina matukar bakin ciki game da rage kudaden kasafin duk shekara domin yana kara muni.
"Wani misali mai tada hankali shi ne, yayin da aka bai wa Ma’aikatar Watsa Labarai Naira Biliyan 2.5 na kashe-kashe 2022, kashi daya cikin uku wanda shine Naira miliyan 869 aka ware don irinsa a kasafin 2023.
"A wurin mu a ma'aikata abin damuwa ne sosai tamkar muna ma'aikatar da gwamnati ta fi datse wa kudi."

Babu Gwamnatin Da Ta Kai Buhari Kokari a Bangaren Gine-Gine a Tarihin Najeriya, Lai Mohammed

Ministan Labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana cewa ginin sabon tashar jirgin saman kasa da kasa ta Murtala Mohammed dake Legas, wani karn hujja ne dake nuna jajircewar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Lai Mohammed ya bayyana hakan ranar Litnin yayin yawon ganin idon da ya kai wajen, ma'aikatar Labarai ta bayyana hakan.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Rantsar da Sabbin Kwamishinoni, Ya Tura Su Ma'aikatun da Zasu Yi Aiki

Asali: Legit.ng

Online view pixel