Ana Saura Kwana 3 Aure, Amarya Ta Fasa Bayan Ango Ya Tsuke Bakin Aljihunsa

Ana Saura Kwana 3 Aure, Amarya Ta Fasa Bayan Ango Ya Tsuke Bakin Aljihunsa

  • Wata budurwa ‘yar Najeriya da ta gaji da jin uzirin saurayinta, ta fasa aurensa ana sauran kwana uku kacal su zama mata da miji
  • Kamar yadda budurwar ta ce, saurayin bai taba zuba ko sisinsa ba a yayin da suke shirin auren kuma a koda yaushe sai yace suna banki
  • Ma’abota amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Facebook masu tarin yawa sun yabawa budurwar inda suka ce ba dole ya iya daukar dawainiyarta ba

Amanda Chisom, ma’abociyar yada labarai ta bayyana labarin wata budurwa wacce ta fasa aure ana sauran kwanaki biyu su zama mata da miji da saurayinta.

Amarya Ta Fasa Aure
Ana Saura Kwana 3 Aure, Amarya Ta Fasa Bayan Ango Ya Tsuke Bakin Aljihunsa. Hoto daga CNN, Adobe Stock Photo
Asali: UGC

A wallafar da aka yi a Twitter, budurwar tace saurayinta ya dinga ce mata kudinsa yana adane a asusun bankinsa wanda zubawa kawai ake yi.

Duk da yadda budurwar ta dinga tambayarsa kudi, saurayin yace zai biya ta duk abinda ta kashe a wurin bikin. Daga bisani kuwa ta fasa auren bayan shawarar da ta samu daga masu bada shawarar aure.

Kara karanta wannan

Matashi Dan Najeriya Ya Nunawa Duniya Kyakkyawar Budurwarsa Farar Fata Tana Rangada Masa Girki a Bidiyo

A kalamanta:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Wannan saurayin bai bani ko kwabo ba kuma aurenmu saura kwana uku, yana cigaba da cewa kudinsa yana asusun bankin da ba a cirewa kuma zai biya ni bayan auren.”

Bashi da komai ne

A yayin martani kan hukuncin budurwar, Amanda tace:

“Mutumin da bashi da sisi, yake rayuwa daga kwano zuwa baki, babu mota, babu gida amma kudinsa na asusun bankin da ba a cirewa. Wannan sakarci ne na karshe wanda za a iya gadonsa.”

Jama’a sun yi martani

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama’a, ga su a kasa:

Vivian Nwuzor tace:

“Gaskiya kin yi abinda ya dace. Asusun bankin da ba a cire kudi shi zai kashe.”

Adeshola Mercy Dada tace:

“Gara da kika yi haka, wannan saurayin ki ‘dan damfara ne.”

Chidinma Faith Mbaekwe tace:

“Ubangiji ne ya kare ki, ki je coci ki bada labari, ya cancanci hakan.”

Kara karanta wannan

Shekaruna 40, Babu Mashinshini Balle In Haihu, Budurwa Ta Koka a Bidiyo

Nkuku-Ogechi Joy Victor yace:

“‘Yar uwa kin tserewa harbin bindiga ne, daga haka ake farawa. Daga nan sai ki fara daukar dawainiya kawu bashi da ko sisi.”

Chinwenma Hope tace:

“Tabbas kin yi daidai! Kin kare kan ki daga mugunta wacce zata iya azabtar da ke.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel