Shekaruna 40, Babu Mashinshini Balle In Haihu, Budurwa Ta Koka a Bidiyo

Shekaruna 40, Babu Mashinshini Balle In Haihu, Budurwa Ta Koka a Bidiyo

  • Wata budurwa ciki da kwarin guiwa ta je soshiyal midiya inda ta nuna damuwarta kan rashin abokin rayuwa.
  • Kamar yadda budurwar mai shekaru 40 a duniya tace, bata da ‘da ko daya na kanta kuma bata ko saurayi a yanzu.
  • Budurwar ta ja hankalin jama’a kan yadda ta dinga jimamiw tare da yi wa kanta jaje, lamarin da yasa jama’a suka dinga karfafa mata guiwa

Wata budurwa mai shekaru 40 a duniya ta jajantawa kanta tare da bayyana cewa bata cikin farin ciki da yanayin da rayuwa ke tafiyar da ita.

A yayin wallafa bidiyonta a TikTok wanda ta bayyana cike da damuwa, budurwar ta rubuta cewa gata nan bata da ‘da balle miji.

Babu Miji
Shekaruna 40, Babu Mashinshini Balle In Haihu, Budurwa Ta Koka a Bidiyo. Hoto daga TikTok Tok/@user5541238600873
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Wata Budurwa Na Neman Saurayi Mara Ko Sisi, Tace Masu Kudi Suna Da Girman Kai, Hotunanta Sun Ja Hankali

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Budurwar mai takaicin yadda rayuwa ke tafiyar da ita ta kara da cewa bata da ko saurayi a halin yanzu kuma tayi kira ga Ubangiji da ya kawo mata dauki.

“Shekaru 40 yanzu, babu ‘da, babu miji kuma babu wata alaka. Oh ni Allah ka kawo min taimako.”

- Ta rubuta a kasan bidiyon da tayi me taba zuciya.

Kalla bidiyon:

Soshiyal midiya tayi martani

Tuni jama’a suka dinga jajanta mata tare da karfafa mata guiwa.

Ga wasu daga cikin martanin:

Lina Lina66158 tace:

“Kada ki cire rai Mama, ina da kawa mai shekaru 48 kuma ta ga ikon Allah. Yanzu haka tayi aure har da yara biyu.”

agmadalo2 tace:

“Kada ki cire rai tawa, duk daya muke da ke. Lokacin da Ubangiji ya zaba mana shi ne daidai.”

Lawon9676yolo yace:

“Allah zai share miki hawayenki kuma ya baki zabin zuciyarki.”

Kara karanta wannan

Bidiyon Saurayi Ya Kaiwa Budurwa Ziyara a Kauye, Yayi Mata Wanki da Diban Ruwa

Secure the bag yace:

“Muna fatan Allah ya baki abinda ki ke so. Ki dai cigaba da imani da Ubangiji.”

Jerrybenzo yace:

“Ina da kawu mai shekaru 47 dake bukatar mace mai shekarun ki, ban sani ba ko kina da ra’ayi. A Legas yake zama.”

Jaydeeomani yace:

“Kada ki cire rai ‘yan mata, shekaru 40 kacal ki ke. Za ki haifa yara. Lokacin da Ubangiji ya zaba shi ne daidai.”

Hotuna: 'Dan Afrika ya kafa tarihin zama mutumin da yafi kowa hangamemen baki a duniya

A wani labari na daban, wani 'dan Afrika ya kafa babban tarihi a duniya bayan ya tabbata mutumin da yafi kowa katon baki a duniya, African Report Files ta ruwaito.

Kamar yadda aka gano, mutumin 'dan asalin kasar Angola kuma hangamemen bakinsa yana daukan gwangwanin kacokan guda daya a bakinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel