Raskwana: Fatima Adamu Maikusa, Yar Arewa Da Ta Lashe Gasar Lissafi Na Kasa da Kasa Har 7

Raskwana: Fatima Adamu Maikusa, Yar Arewa Da Ta Lashe Gasar Lissafi Na Kasa da Kasa Har 7

  • Fatima Adamu Maikusa, matashiyar yar Najeriya ce wacce ta kware wajen buga lissafi tamkar na’ura mai kwakwalwa
  • Matashiyar mai shekaru 14, wacce haifaffiyar yar jihar Gombe ce ta fara lashe gasar lissafi tun tana yar shekaru tara a duniya
  • A yanzu haka Fatima na da lambar yabo na kasa da kasa guda daddaya har 7 da ta lashe a gasar lissafi

Wata matashiyar budurwa yar Najeriya mai suna Fatima Adamu Maikusa, ta burge jama’a da dama saboda tarin baiwar da Allah yayi mata na iya lissafi sai kace na’ura mai kwakwalwa.

Fatima mai shekaru 14 ta kasance haifaffiyar yar jihar Gombe da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Fatima
Raskwana: Fatima Adamu Maikusa, Yar Arewa Da Ta Lashe Gasar Lissafi Na Kasa da Kasa Har 7 Hoto: @InsideKaduna_.
Asali: Twitter

An fara damawa da ita a gasar lissafi tun tana da shekaru tara a duniya inda ta fara da lashe gasar lissafi na Amurka (AMC 08).

Kara karanta wannan

Wani Aiki Sai Mallam: Nasir El-Rufa'i Ya Koma Kwashe awanni 9 Jere Yana Bada Darasi

Shafin @InsideKaduna_ wanda ya wallafa labarin a Twitter ya ce matashiyar ta lashe lambar yabo daddaya har guda bakwai a gasar lissafi na kasa da kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yanzu haka, tana karatunta ne a kwalejin mata na NTIC Kano da ke jihar Kano.

Ga jerin gasar da Fatima ta lashe:

  1. Gasar lissafi na Amurka (AMC 08)
  2. Gasar ilimin lissafi na kasa da kasa da aka gudanar a Jakarta, babban birnin kasar Indonesia
  3. Gasar lissafi na kasa da kasa da aka yi a Bangkok, kasar Thailand
  4. Gasar lissafi na kangourou sans frontiers-KSF
  5. Gasar hazikan dalibai na FISO
  6. Gasar lissafi na Bulgaria
  7. Bikin lissafi na Komodo, Indonesia.

Jama'a sun yi martani

@chukwura_a ta yi martani:

“Kada ku je ku aurar da ita ku barta ta cimma burinta wanda ka iya kawo sauyi a duniya.. a yiwa matanmu na arewa adalci.”

Kara karanta wannan

2023: Tinubu, Obi ko Atiku? Bincike Ya Nuna Wanda Zai Ci Zaɓen Shugaban Ƙasa, An Bayyana Abin Da Zai Faru

@Great_51432 ya yi martani:

"Ma Sha Allah."

@AbdulbasitIsha8 ya ce:

“Hakan ya yi kyau.”

Gidauniyar Bashir Ahmad Ta Dauki Nauyin Karatun Yarinya Mai Baiwar Lissafi Tun Daga Firamare Har Zuwa Jami’a

A wani labarin kuma, mun ji cewa Allah ya tarbawa garin wata karamar yarinya yar asalin jihar Kano nono, inda ta samu tallafin karatu kyauta tun daga Firamare har zuwa jami’a.

Saratu Dan-Azumi kamar yadda aka bayyana sunanta, ta kasance hazikar yarinya wacce Allah ya yiwa baiwar hada lissafi duk da karancin shekarunta.

Gidauniyar tsohon mai baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin sadarwar zamani, Bashir Ahmad ne ya dauki nauyin karatun Saratu bayan ya samu yardar mahaifanta.

Ahmad ya bazama neman yarinyar da iyayenta ne tun bayan da ya ci karo da bidiyonta wanda ke ta yawo a shafukan soshiyal midiya inda ake mata tambayoyi masu zurfi a bangaren lissafi kuma tana bayar da amsa daidai.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC Tayi Nasarar Daure 'Yan Damfara 2, 800 a Watanni 10 a 2022

Asali: Legit.ng

Online view pixel