Nasir El-Rufa'i Ya Koma Malamin Aji: Ya Kwashe awanni 9 Jere Yana Bada Darasi

Nasir El-Rufa'i Ya Koma Malamin Aji: Ya Kwashe awanni 9 Jere Yana Bada Darasi

  • Gwamnan jihar Kaduna kuma jigo jam'iyyar All Progressives Congress ya nuna cewa ko ba siyasa akwai wajen neman abinci
  • Hotuna sun bayyana lokacin da Gwamnan ke zubawa daliban Kashim Ibrahim Fellowship karatu
  • Yan Najeriya sun bazama kafafen sadarwa don tofa albarkatun bakinsu kan wannan lamari

Kaduna - Gwamna Nasir Ahmed El-Rufa'i na jihar Kaduna ya shiga aji karantar da daliban Kashim Ibrahim Fellowship kan muhimmancin shugabanci da tattalin arziki.

A labarin da Kashim Ibrahim Fellowship KIF ya saki a shafinsa na Tuwita, yace gwamnan ya gudanar da warsha kan tsarin shirye-shirye na McKinsey’s 7-S.

Yace:

"Sa'o'i tara aka kwashe ana yi yayi kyau."
"Ajin Phoenx yau ya zauna da mai girma gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i don karatu kan iya mulki da tattalin arziki."

Kara karanta wannan

2023: Tinubu, Obi ko Atiku? Bincike Ya Nuna Wanda Zai Ci Zaɓen Shugaban Ƙasa, An Bayyana Abin Da Zai Faru

"Mallam ya karantar da dalibai sosai kan McKinsey’s 7-S Framework, wani na'ura mai karfi wajen tsare-tsare, shirye-shirye da bincike."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Dalibai sun koyi ilimin mulkin kasa, abubuwa uku da ake amfani da su wajen tsara kasa, da kuma alakar karfin mulki da al'umma."
Malam
Nasir El-Rufa'i Ya Koma Malamin Aji: Ya Kwashe awanni 9 Jere Yana Bada Darasi Hoto: @KDSG_KIF
Asali: Facebook

Shirin Kashim Ibrahim Fellowship

Kashim Ibrahim Fellowship (KIF) wani tsari ne na shekara daya do horar da matasa yan shekara 25 zuwa 35 kan shugabanci.

Shirin na da manufar ilmantar da matasan Najeriya da ake sa ran zasu hau gadon mulki wata rana a gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel