Zanga Zanga Ta Barke A Unguwar Yan Sanda Kan Barazanar Tsaro A Abuja
- Mazauna rukunin gidajen yan sanda na Kurudu sun yi zanga-zanga a kofar shiga unguwar kan barazanar tsaro a unguwar
- Masu zanga-zangar sun yi zargin cewa wanda aka bawa kwangilar gini a unguwar yana saba dokoki kuma sun koka kan rashin ababen more rayuwa
- Mutanen unguwar sun ce an rubuta a kalla wasiku 30 ga IGP na yan sanda ta hannun kwamishinan yan sanda, amma ba a dauki matakin magance fashi da ake yi a unguwar ba
FCT Abuja - A yayin da ake fargabar harin ta'addanci a Abuja, mazauna rukunin gidajen yan sanda na Kurudu a Abuja sun yi zanga-zanga kan abin da suka kira karuwar barazanar tsaro da yan fashi ke musu, da saba ka'idar gini da rashin ababen more rayuwa.
A cewar The Nation, masu zanga-zangar sun rufe kofar shiga unguwar yan sandan a ranar Asabar, 29 ga watan Oktoba. Sun hana motocci shiga ko fita daga unguwar don isar da sakonsu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sun dauki takardu masu rubuce-rubuce, suna kira ga ministan Abuja, Muhammad Bello da Sufeta Janar Na Yan Sanda, Usman Baba su saka baki.
Mutane na zaman dar-dar a Abuja, da kewaye kan yiwuwar kawo harin ta'addanci da wasu kasashe suka yi gargadi, har suka shawarci mutanensu su bar Abuja.
Me yasa mutane ke zanga-zanga a Abuja
Masu zanga-zangar kuma suna rera wakokin nuna rashin gamsuwarsu.
Daya daga cikin masu zanga-zangar kuma mataimakin shugaban masu gidaje a kurudu police estate, Oregbesan Olakekan, ya ce mutanen unguwar sun rubuta a kalla wasiku 30 ga IGP ta ofishin kwamishinan yan sanda amma ba su ga an dauki wani mataki ba.
Olalekan ya bayyana cewa yan fashi suna damun mutanen unguwar yayin da ya ke zargin wanda aka kwangilar ginin ba ya abin da ya dace.
Ba Sojojin Amurka Ne Suka Kai Samame A Abuja Ba, In Ji Mazaunin Unguwa
A wani rahoton, kun ji cewa sojojin Amurka ba su cikin wadanda suka kai samame a rukunin gidaje na Trademore da ke Lugbe, babban birnin tarayya, Abuja, in ji wani mazaunin unguwar, Daily Trust ta rahoto.
Mazaunin, wanda ya tabbatar an kawo samame unguwar, ya ce kawai dan kasar waje daya aka gani cikin jami'an da suka kawo samamen.
A hirar da ya yi da Daily Trust a ranar Laraba, kakakin yan sandan Abuja, Josephine Adeh, ta ce mazauna unguwar ba su sanar da rundunar game da lamarin ba.
Asali: Legit.ng