Fargabar Hari: Bayan Jabi Lake Mall, Wani Babban Kamfani Ya Sake Rufe Ayyukansa A Abuja
- Kamfanin gine-gine na Julius Berger ya rufe ayyukansa a birnin tarayya Abuja saboda tsaro
- Julius Berger ta kuma shawarci ma'aikatanta su guji zuwa wuraren taruwar mutane kamar kanti, kulob, otel da sauransu
- A yan kwanakin nan ne babban kanti na Jabi Lake Mall ya rufe ayyukansa biyo bayan gargadin kawo hari a Abuja daga kasar Amurka
FCT Abuja - Kamfanin gine-gine na Julius Berger ya rufe ayyukansa a babban birnin tarayya Abuja, The Punch ta rahoto.
Rufewan na zuwa ne a matsayin martani kan fargabar harin ta'addanci a babban birnin tarayya da tsakiyar Abuja.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cikin sanarwar da kamfanin ta fitar a ranar Asabar, ta shawarci ma'aikatanta su guji zuwa wuraren taruwar mutane a yayin karshen mako.
2023: Tinubu, Obi ko Atiku? Bincike Ya Nuna Wanda Zai Ci Zaɓen Shugaban Ƙasa, An Bayyana Abin Da Zai Faru
Ta kara da cewa za ta duba yiwuwar yin kaura na wucin gadi zuwa wasu wuraren.
Sanarwar:
"Ana bada shawawar a kaurace wa wuraren taruka a Abuja da kewaye, ciki har da kanti, wuraren cin abinci, otel, wuraren shan giya, kulob da wasu wurare da mutane da yawa ke taruwa. Wannan zai fara aiki daga ranar 28/10/2022 da yamma har zuwa ranar Litinin, 31/10/2022 da safe.
"Akwai yiwuwar a yi kaura zuwa wuraren aiki na JBN ko wasu gidaje a karshen mako.
"Lafiyar ku shine abu mafi muhimmanci gare mu."
Tunda farko, Legit.ng Hausa ta rahoto cewa wani kanti ya rufe bayan gargadin kawo harin ta'addancin.
Manyan Kantunan Abuja Sun Fara Rufewa Sakamakon Labarin Cewa Za'a Kai Hari
Babban kantin Jabi Lake Mall da ke unguwar Utako a birnin tarayya Abuja ta rufe dukkan shagunanta ranar Alhamis sakamakon barazanar tsaron da ake yiwa garin.
A jawabin da kantin ya daura a shafinsa na Instagram @jabilakemallnigeria, hukumomin sun bayyana cewa duk da cewa ba tada niyyar tadawa mutane hankali, sun yanke shawaran haka ne domin kare rayukan masu zuwa siyayya da ma'aikatanta.
Sun kara da cewa suna bibiyan yadda alamarin ke gudana kuma idan komai ya daidaita za'a bude.
Asali: Legit.ng