Kada A Saki Nnamdi Kanu, Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Sabon Hukunci

Kada A Saki Nnamdi Kanu, Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Sabon Hukunci

  • Bayan nasarori biyu da ya samu kan gwamnati a baya, Nnamdi Kanu ya sake fuskantar cikas ga yancinsa
  • Kotun daukaka kara ta ce kada a sake shi sai kotun koli ta yanke shawarar karshe kansa
  • Gwamnatin Buhari a shekarar 2021 ta sankamo Nnamdi Kanu daga kasar Kenya inda ya tafi harkoki

Kotun daukaka kara a ranar Juma'a ta amince da bukatar gwamnatin tarayya na hana aiwatar da dokar babbar kotun tarayya ta ranar 13 ga Oktoba cewa a saki Nnamdi Kanu.

Alkali Haruna Tsammani wanda ya yanke hukuncin ya bada umurnin cewa a tafi kotun koli cikin kwanaki bakwai don a yanke hukuncin karshe, rahoton ChannelsTV.

Hakan na nufin cewa za'a cigaba da rike Nnamdi Kanu a magarkamar hukumar tsaron farin kaya DSS har sai kotun kolin ta yanke hukunci.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ana Tsaka Da Fargabar Hari, Mota Ta Kama Da Wuta A Kusa Da Ma'aikatar Shari'a A Abuja

Alkalin yayin yanke hukunci yau yace takardar da lauyoyin Kanu suka shigar don kawar da gwamnatin tarayya ba su kamshin gaskiya.

Nnamdi Kanu
Kada A Saki Nnamdi Kanu, Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Sabon Hukunci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu Ta Umurci Gwamnatin Tarayya Ta Biya Nnamdi Kanu N500m Kuma A Mayar Da Shi Kenya

Babbar kotun tarayya dake zamanta a Umuahia, jihar Abia ta umurci gwamnatin tarayya ta mayar da Nnamdi Kanu inda suka dauko shi a kasar Kenya a watan Yunin 2021.

Nnamdi Kanu shine shugaban kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra IPOB.

Bugu da kari, kotu ta umurci gwamnati ta biya Kanu kudi N500 million a matsayin garkuwa da shi da gwamnati tayi da kuma take masa hakki na bil adama.

Kotu Ta Wanke Nnamdi Kanu Amma Bata Ce Mu Sakeshi ba, AGF Malami

Antoni-Janar na tarayya kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, a ranar Alhamis ya yi tsokaci kan hukuncin kotun daukaka kara da ta wanke Nnamdi Kanu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Gwani Alkali Yayi Nasara a Zaben Jos North

Nnamdi Kanu shine jagoran kungiyar rajin kafa kasar Biyafara watau IPOB.

A jawabin da mai magana da yawunsa, Dr. Umar Jibril Gwandu, ya fitar, Mr Malami ya ce kawai kotu ta wanke Kanu ne amma bata ce a sakeshi

Yace:

"Ofishin Antoni Janar na tarayya kuma Ministan Shari'a ta samu labarin kotun daukaka kara game da Nnamdi Kanu."
"Amma fa a sani, kawai an wanke Kanu ne amma ba'a sake shi ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel