Ana Tsaka Da Fargabar Hari, Mota Ta Kama Da Wuta A Kusa Da Ma'aikatar Shari'a A Abuja

Ana Tsaka Da Fargabar Hari, Mota Ta Kama Da Wuta A Kusa Da Ma'aikatar Shari'a A Abuja

  • Wata mota kira Hilux ta kama da wuta kusa da ginin Ma'aikatar Sharia kan Dalaba Street, Wuse Zone 5, Abuja a ranar Juma'a, 28 ga watan Oktoba
  • Duk da cewa kawo yanzu ba a san sanadin konewar motar ba, an rahoto cewa motar ta yi mummunan konewa ba a iya gane ta
  • Ba tare da rasa rai ba, an kashe gobarar yayin da jami'in hukumar kiyayye haddura, FRSC, suka kawar da motar don rage cinkoso

FCT, Abuja - An shiga firgici a ranar Juma'a, 28 ga watan Oktoba, kusa da Dalaba Street, Wuse Zone 5, Abuja, inda Ma'aikatar Shari'a ta ke, saboda kama wuta da wata motar kirar Hilux ta yi.

An tattaro cewa motar kwatsam da kama da wuta a babban hanyar, hakan ya jefa ma'aikata, masu wucewa, da masu ababen hawa cikin tsananin tsoro, The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Dan a mutun Peter Obi ya samu lambar yabo a kasar Tanzania bayan kafa tura a Kilimanjaro

Hilux
Ana Tsaka Da Fargabar Hari, Mota Ta Kama Da Wuta A Kusa Da Ma'aikatar Shari'a A Abuja. Hoto: Sahara Reporters.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sahara Reporters ta rahoto cewa wutar ya shafe mintuna yana ci kuma ya yi wa motar barna sosai kafin masu motocci a kusa suka yi kokarin kashe wutar da na'uarar kashe gobara.

Bayan dan wani lokaci, yan kwana-kwana da jami'an hukumar kiyayye haddura na kasa, FRSC, sun zo wurin suka kashe gobarar.

A yayin da aka kawar da konaniyar Hilux din gefen titi, abubuwa sun fara daidaituwa a yankin.

Ba Sojojin Amurka Ne Suka Kai Samame A Abuja Ba, In Ji Mazaunin Unguwa

A wani rahoton, kun ji cewa sojojin Amurka ba su cikin wadanda suka kai samame a rukunin gidaje na Trademore da ke Lugbe, babban birnin tarayya, Abuja, in ji wani mazaunin unguwar, Daily Trust ta rahoto.

Mazaunin, wanda ya tabbatar an kawo samame unguwar, ya ce kawai dan kasar waje daya aka gani cikin jami'an da suka kawo samamen.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS da NIA Sun Damke Yan Ta'addan ISWAP 35 A FCT Abuja

A hirar da ya yi da Daily Trust a ranar Laraba, kakakin yan sandan Abuja, Josephine Adeh, ta ce mazauna unguwar ba su sanar da rundunar game da lamarin ba.

Adeh, mataimakiyar sufritandan yan sanda, kuma ta ce 'labarin karya ne' rahoton da ke ikirarin jami'an DSS da sojojin Amurka sun gano akwatunan abubuwa masu fashewa a unguwar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel