Kotun Daukaka Kara Ta Fitittiki Dan Majalisar PDP Na Jos North, Ta Tabbatar Da Gwani Alkali Yayi Nasara

Kotun Daukaka Kara Ta Fitittiki Dan Majalisar PDP Na Jos North, Ta Tabbatar Da Gwani Alkali Yayi Nasara

  • Dan takarar kujerar majalisar wakilai karkashin PRP, Gwani Adam Alkali, ya yi nasara a kotu karshe
  • Kotun ta yi kira ga hukumar INEC ta yi gaggawar mika takardar shaidar nasara a zabe ga Gwanin na Al-Qur'ani
  • Gwani Adam Alkali zai wakilci Jos/Bassa ana saura watanni biyar sabon zabe na Maris 2023

Jos - Kotun daukaka karar dake yankin Jos, jihar Plateau a ranar Juma'a ta yanke hukuncin karshe kan zaen kujeran dan majalisa mai wakiltar mazabar Jos North/Bassa.

Alkalin kotun ya tabbatar da Hon Muhammad Alkali Goni na jam'iyyar People’s Redemption Party(PRP) matsayin wanda yayi nasara, rahoton TheNation.

Kotun ta yi watsi da karar Hon. Musa Agah Avia na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Kotun ta umurci hukumar zabe ta INEC ta baiwa Alkali Goni kwalin shaidar nasara a zaben kuma a rantsar da shi kai tsaye.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ana Tsaka Da Fargabar Hari, Mota Ta Kama Da Wuta A Kusa Da Ma'aikatar Shari'a A Abuja

Da dumi
Kotun Daukaka Kara Ta Fitittiki Dan Majalisar PDP Na Jos North, Ta Tabbatar Da Gwani Alkali Yayi Nasara
Asali: Original

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Nasarar Farko

A ranar 2 ga Satumba, Kotun zaben majalisar dokoki dake zamanta a kotun High Court 4, Jos a ranar Juma'a ta fitittiki Musa Avia Aggah, dan majalisar wakilan tarayya na jam'iyyar PDP.

Musa Avia Aggah ya kasance mai wakiltar mazabar Jos ta Arewa da Bassa a majalisar wakilai.

Kotun ya bayyana cewa ba Agah bane halastaccen wanda ya lashe zaben fidda gwanin PDP a zaben, rahoton TheNation.

Kotu tace Agah bai lashe zaben ba, magudi aka yi.

A hukuncin da Alkalan kotu Justice Hope O. Ozoh. Khadi Usman Umar, da Justice Zainab M. Bashir, suka yanke, lauyoyin Gwani Alkali sun tabbatar da gaskiya.

Saboda hakan, kotun ta alanta Goni Muhammad Adam Alkali na jam'iyyar People Redemption Party (PRP), matsayin wanda yayi nasara

Sakamakon zaben cike gibi

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Ba Wa Cocin Katolika Kyautan Naira Miliyan 20 A Wata Jihar Arewa

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), ta ayyana Hon. Musa Agah na jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na dan majalisar tarayya mai wakiltan Jos ta Arewa/Bassa.

INEC ta bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 27 ga watan Fabrairu, 2022.

Baturen zabe, Dr Oyeyinka Oyerinda, ya sanar da cewar Agah ya samu kuri’u 40, 343 wajen kayar da dan takarar jam’iyyar PRP, Hon. Muhammad Gwani, wanda ya samu kuri’u 37, 757.

Hon. Abbey Aku na jam’iyyar All Progresives Congress (APC) mai mulki ya samu kuri’u 26,111.

Asali: Legit.ng

Online view pixel