Kotu Ta Fitittiki Dan Majalisar Wakilan PDP Na Jos North, Tace Goni Alkali Yayi Nasara

Kotu Ta Fitittiki Dan Majalisar Wakilan PDP Na Jos North, Tace Goni Alkali Yayi Nasara

  • Dan takarar kujerar majalisar wakilai karkashin PRP, Gwani Adam Alkali, ya yi nasara a kotu
  • Kotun ta yi kira ga hukumar INEC ta kwace takardar shaidar nasara a zabe daga hannun dan jam'iyyar PDP
  • Idan dan majalisar bai tafi kotun daukaka kara ba, Gwani Adam Alkali zai wakilci Jos/Bassa ana saura watanni biyar zabe

Jos - Kotu zaben majalisar dokoki dake zamanta a kotun High Court 4, Jos a ranar Juma'a ta fitittiki Musa Avia Aggah, dan majalisar wakilan tarayya na jam'iyyar PDP.

Musa Avia Aggah ya kasance mai wakiltar mazabar Jos ta Arewa da Bassa a majalisar wakilai.

Kotun ya bayyana cewa ba Agah bane halastaccen wanda ya lashe zaben fidda gwanin PDP a zaben, rahoton TheNation.

Kotu tace Agah bai lashe zaben ba, magudi aka yi.

Kara karanta wannan

2023: Za A Gwabza Zabe Mai wahalan Da Ba A Taba Yin Irinsa Ba A Tarihin Najeriya, Inji APC

A hukuncin da Alkalan kotu Justice Hope O. Ozoh. Khadi Usman Umar, da Justice Zainab M. Bashir, suka yanke, lauyoyin Gwani Alkali sun tabbatar da gaskiya.

Saboda hakan, kotun ta alanta Goni Muhammad Adam Alkali na jam'iyyar People Redemption Party (PRP), matsayin wanda yayi nasara, riwayar Daily Trust.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Agah Via
Kotu Ta Fitittiki Dan Majalisar Wakilan PDP Na Jos North/Bassa
Asali: Facebook

Sakamakon zaben cike gibi

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), ta ayyana Hon. Musa Agah na jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na dan majalisar tarayya mai wakiltan Jos ta Arewa/Bassa.

INEC ta bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 27 ga watan Fabrairu, 2022.

Baturen zabe, Dr Oyeyinka Oyerinda, ya sanar da cewar Agah ya samu kuri’u 40, 343 wajen kayar da dan takarar jam’iyyar PRP, Hon. Muhammad Gwani, wanda ya samu kuri’u 37, 757.

Kara karanta wannan

INEC Ta Sanar Da Ranar Wallafa Ta Karshe Na Sunayen Dukkan Yan Takara A Zaben 2023

Hon. Abbey Aku na jam’iyyar All Progresives Congress (APC) mai mulki ya samu kuri’u 26,111.

Asali: Legit.ng

Online view pixel