Tinubu Ya Bawa Cocin Katolika Kyautan Naira Miliyan 20 A Wata Jihar Arewa

Tinubu Ya Bawa Cocin Katolika Kyautan Naira Miliyan 20 A Wata Jihar Arewa

  • Cocin Katolika ta St Francis da ke Otukpo ta samu tallafin kudi Naira miliyan 20 daga Bola Tinubu
  • Dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar APC a zaben 2023 ya bada tallafin ne a yayin da cocin ke bikin cikarta shekara 100
  • Tinubu ya kuma taya fastoco da ma'aikatan coci da sauran mambobin cocin murnar wannan biki

Otukpo - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya bada Naira miliyan 20 ga cocin katolika da ke jihar Benue, rahoton Legit.ng.

Rabaran Hyacinth Alia, dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Benue ne ya gabatar da kyautar ta Tinubu a bikin cikar cocin shekaru 100 a Otukpo.

Tinubu
Bola Tinubu Ya Bawa Cocin Katolika Kyautan Naira Miliyan 20 A Wata Jihar Arewa. Hoto: (@OfficialBAT)
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

"Ku Yi Hattara Da Mayaudaran Ƴan Siyasa", APC Ta Aikewa Ƴan Najeriya Sako Mai Ƙarfi A Gabanin Zaɓen 2023

Wata sanarwa da hadimin Alia a bangaren watsa labarai, Isaac Uzaan ya fitar a ranar Alhamis, 27 ga watan Oktoba ta ce Tinubu yana taya fastoci, ma'aikata da dukkan mambobin cocin murnar wannan bikin.

Ya lura cewa cocin ta yi shekaru 100 tana dagewa wajen yada bisharar ceto a Najeriya, musamman ga mutanen Benue ta Kudu.

Dan takarar shugaban kasa na APC ya bayyana fatansa cewa idan aka dage da addu’a da ayyuka masu kyau kasar za ta shawo kan kalubalen da ke adabarta.

Kazalika, ministan ayyuka na musamman, Sanata George Akume ya bawa cocin kyautan Naira miliyan 10.

Akume wanda jagoran APC ne a Benue kuma tsohon gwamnan jihar, ya samu wakilcin shugaban APC na jihar, Mr Austin Adaga.

Ya bukaci mutanen jihar su dage wurin addu'o'i ga jihar da Najeriya don ta shawo kan kallubalen da suke adabatarta.

2023: Ɗaliban Najeriya Sun Goyi Bayan Takarar Tinubu Da Shettima, Sun Bada Ƙwakwarar Dalili

Kara karanta wannan

Musulmi da Kirista duk daya ne: Tinubu ya yiwa malaman addini jawabi a Kano

Shugaban kungiyar Tinubu/Shettima Vanguard na kasa, Mr Sunday Asefon, a ranar Laraba 26 ga watan Oktoba, a Abuja, ya yi alkawarin tattaro kan daliban Najeriya zu zabi Tinubu Shetima a zaben shugaban kasa na 2023.

Asefon ya yi wannan alkawarin ne yayin kaddamar da kungiyar Tinubu/Shettima Vanguards, The Nation ta rahoto.

Asefon, tsohon shugaba na kasa na kungiyar daliban Najeriya, (NANS), ya ce kungiyar za ta zama babban tafiya ta dalibai da zata taimaka wurin tabbatar da nasarar 'Renewed Hope'.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel