Amurka Ta Shawarci Ma'aikatan Ofishinta Su Kwashe Iyalansu Daga Abuja Yanzu

Amurka Ta Shawarci Ma'aikatan Ofishinta Su Kwashe Iyalansu Daga Abuja Yanzu

  • Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa lamarin yunkurin kai hari Abuja na kari kamari saboda ma'aikatanta su kwashe iyalansu
  • Gwamnatin tarayya ta ce yan Najeriya su kwantar da hankulansu game da labarin cewa za'a kai hari Abuja
  • Gwamnatin Amurka da ta Burtaniya sun gargadi 'ya'yansu mazauna Najeriya da su kula matuka kan yiwuwar samun hare-hare

Abuja - Yayinda ake barazanar harin yan ta'addan a birnin tarayya Abuja, Gwamnatin Amurka ta bukaci iyalan ma'akatansu dake zama a Abuja su bar birnin da gaggawa.

Wannan na kunshe cikin sabon shawaran da ofishin jakadancin Amurka dake Najeriya ya fitar.

Wannan ya biyo bayan jawabin Amurka na cewa shirya take da ta fara kwashe yan kasarta dake Najeriya.

A cewar jawabin:

Kara karanta wannan

An samu karin kasashe da suka gano yiwuwar kai hare-hare a Abuja da Jihohi 22

"Mun yi karin bayani kan lamarin barazanar hari a Abuja. Muna baiwa yan kasar Amurka kada suyi tafiya Abuja yanzu."
"Hakazalika ranar 27 ga Oktoba, 2022, an umurci iyalan ma'aikata gwamnatin Amurka dake Abuja su fita daga Abuja saboda tsoron hari."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Yan Amurka su nemi motar haya su fita daga Abuja. Wadanda basu samu motar haya ba su tuntubi ofishin jakadancin Amurka dake Legas don taimako."
Embassy
Amurka Ta Shawarci Ma'aikatan Ofishinta Su Kwashe Iyalansu Daga Abuja Yanzu
Asali: UGC

Babban Kanti A Abuja Ta Rufe Shagunanta Sakamakon Labarin Cewa Za'a Kai Hari

Babban kantin Jabi Lake Mall dake unguwar Utako a birnin tarayya Abuja ta rufe dukkan shagunanta ranar Alhamis sakamakon barazanar tsaron da ake yiwa garin.

A jawabin da kantin ya daura a shafinsa na Instagram @jabilakemallnigeria, hukumomin sun bayyana cewa duk da cewa ba tada niyyar tadawa mutane hankali, sun yanke shawaran haka ne domin kare rayukan masu zuwa siyayya da ma'aikatanta.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Atiku Ya Dira Birnin Amurka Don Yakin Neman Zabe

Sun kara da cewa suna bibiyan yadda alamarin ke gudana kuma idan komai ya daidaita za'a bude.

Kuyi Watsi Da Maganar Amurka, Najeriya Tafi Zaman Lafiya Yanzu: Lai Mohammed

Ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana cewa Najeriya ta fi zaman lafiya yanzu fiye da kowani lokaci a shekarun baya-bayan nan.

Lai ya bayyana hakan a tattaunawar da yayi a taron UNESCO da ya gudana a birnin tarayya Abuja ranar Talata, rahoton TheCable.

Ya yi martani ne game da gargadin da gwamnatin Amurka da Birtaniya tayi na cewa da yiwuwan yan bindiga su kai hari birnin tarayya Abuja.

Ya tuhumci yan jarida da zuzuta lamarin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel