'Rabon Shinkafa' Ba Karfafawa Matasa Gwiwa Bane, Shahararren Gwamnan Najeriya Ya Faɗa Wa Ƴan Siyasa

'Rabon Shinkafa' Ba Karfafawa Matasa Gwiwa Bane, Shahararren Gwamnan Najeriya Ya Faɗa Wa Ƴan Siyasa

  • Farfesa Chukwuma Soludo, gwamnan jihar Anambra ya ce rabon buhunan shinkafa da yan siyasa ke wa matasa ba karfafa gwiwa bane
  • Soludo ya ce rabawa mutane kayan abinci sadaka ne kawai kuma bayan sun cinye za su nemi abinci a gobe
  • Tsohon shugaban babban bankin na kasa, CBN, ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali ne wurin koyar da sana'o'i don matasa su rike kansu

Anambra - Gwamnan Jihar Anambra Farfesa Charles Soludo ya bayyana ayyukan tallafi da wasu yan siyasa a jihar ke yi a matsayin 'sadaka ga mabukata'.

A cewar Soludo, rabawa matasa buhunan shinkafa ba karfafawa bane, kawai dai sadaka ne na kayan abinci, rahoton Daily Trust.

Gwamna Soludo
'Rabon Shinkafa' Ba Tallafawa Matasa Bane, Gwamna Mai Karfin Fada Aji Ya Fada Wa Yan Siyasa. Hoto: @daily_trust.
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Fitaccen Gwamnan Najeriya Ya Janye Harajin Da Ya Kakabawa Masu Talla, Masu Tura Baro Da Masu Faci A Jiharsa

Gwamnan ya yi wannan jawabin a wurin kaddamar da taron koyar da sana'a na rana guda mai lakabin 'One Youth, Two Skills Solution".

Kama kifi za mu koya muku, a maimakon baku kifi - Soludo

Shirin, wanda Ma'aikatar Matasa na Jihar Anambra ta yi a Cibiyar International Convention Centre da ke Awka an masa lakabi ne da; "Samar da fasihan masu sana'o'i don bunkasa jihar Anambra."

Soludo ya ce:

"Mun taho domin fara shirin karfafa gwiwa ta yadda za mu koya muku kama kifi, maimakon baku kifi.
"Yan siyasa da sauran mutane suna yin abin da na ke kira sadaka ga mabukata; raba buhunan shinkafa ga matasa na karfafawa bane amma ba su abinci na kwana guda kuma gobe za su ji yunwa.
"Za mu baku horaswa. Shirin mu shine mu koyar da kowanne matashi a kalla sana'a biyu. Wannan shine hangen nesan da muke wa Anambra, Najeriya da Afirka."

Kara karanta wannan

Rudani: Gwamnan PDP mai ba Atiku ciwon kai ya zabo tsohon jigon APC ya zama kwamishinansa

Gwamnan ya kara da cewa zai sake fitar da kudade a shekaru masu zuwa domin tsare-tsaren koyar da matasa sana'o'i.

Fitaccen Gwamnan Najeriya Ya Janye Harajin Da Ya Kakabawa Masu Talla, Masu Tura Baro Da Masu Faci A Jiharsa

A wani rahoton, Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya yi mi'ara koma baya ya soke dukkan harajin da ya saka wa masu tura amalanke, kanikawa, masu talla da sauran ma'aikata a jihar.

Gwamnan ya bada umurnin ne yayin jawabin da yi wa mutanen Anambra a taron hanyoyin samun haraji karo na biyu a gidan gwamnati a Awka, rahoton Daily Trust.

A cewar Soludo, masu talla, masu tura amalanke da baro, da kanikawa ba su cikin wadanda za su biya harajin a Jihar Anambra.

Asali: Legit.ng

Online view pixel