Gobara Ta Tashi A Ofishin WAEC, Ana Fargabar Mutane Da Dama Sun Makale A Ciki

Gobara Ta Tashi A Ofishin WAEC, Ana Fargabar Mutane Da Dama Sun Makale A Ciki

  • Gobara ta tashi a hedkwatar ofishin hukumar shirya jarrabawa ta Afirka ta yamma, WAEC da ke Jihar Legas
  • Hukumar bada agajin gaggawa na Legas, LASEMA, ta ce karuwar wutar lantarki a wani sashi na ginin ya janyo gobarar
  • Ma'aikatan hukumar mata guda bakwai sun makale a ginin, amma daga bisani an ceto su an kuma kashe wutar

Legas - Wani sashi na ginin hedkwatar hukumar shirya jarrabawa ta WAEC da ke Jibowu Legas ya kama da wuta, The Cable ta rahoto.

Gobara a ofishin WAEC a Legas
Gobara Ta Tashi A Ofishin WEAC, Ana Fargabar Mutane Da Dama Sun Makale A Ciki. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Sanadin gobarar a ofishin WAEC a Legas

Hukumar bada agajin gaggawa na jihar Legas, LASEMA, a ranar Laraba ta ce 'karuwar karfin wutar lantarki' a bene na uku a gidan ya janyo gobarar.

An ceto mutane bakwai da suka makale a ginin

Hukumar ta ce ma'aikata mata bakwai sun makale a bena na biyar da bakwai na ginin - amma daga bisani an fito da su.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: INEC ta ware jihohi 3 da za su yi zaben gwamnan 2023 a wani lokaci daban

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

LASEMA a sanarwar da ta bada kan lamarin ta ce:

"Da isar mu wurin da aka ambata, an gano wani sashin ginin hedkwatar WAEC na ci da wuta.
"Karin binciken da aka yi ya nuna cewa wutar ta tashi ne a bene na uku na ginin mai bene 12 saboda karuwar wutar lantarki.
"Ma'aikata mata bakwai na hukumar ne suka makale a bene na biyar da bakwai kuma an yi nasarar ceto su bisa kokarin tawagar ceto da suka isa wurin. An kuma kashe wutar ta mutu.
"Jami'an hukumar mu tare da masu bada agajin gaggawa, LASG FIRE, FED FIRE, UNILAG FIRE, LASAMBUS da LASTMA suna can don tabbatar da samar da daidaito cikin gaggawa."

Hukumar ta kara da cewa ana can ana aikin tabbatar da komai ya koma daidai.

Bauchi: Mummunan Gobara Ta Lakume Shaguna 42 a Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa

Kara karanta wannan

Karin Bayan: Manhajar WhatsApp Ta Dawo Aiki Bayan Daina Aiki

A wani rahoton, a kalla shaguna 42 ne suka kone a Student Centre, ta Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi, sakamakon gobara da ta yi sanadin asarar dukiyoyin miliyoyin naira.

Shagunan da suka kone a Block D suna bayan dakin kwanan dalibai mata ne a Yelwa Campus na jami'ar kamar yadda The Punch ta rahoto.

Shagunan da gobarar ta yi wa barna sun hada da shagunan kwamfuta, shagunan aski a shagunan sayar da kayan masarufi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel