Gwamnan Najeriya Ya Rufe Dukkan Gidajen Caca Da Wasanni A Jiharsa, Ya Bada Dalili Mai Karfi

Gwamnan Najeriya Ya Rufe Dukkan Gidajen Caca Da Wasanni A Jiharsa, Ya Bada Dalili Mai Karfi

  • An dakatar da dukkan gidajen caca da buga gyam a jihar Anambra biyo bayan umurnin gwamnan jihar
  • Gwamnatin na Anambra ta ce ta samu rahoto mai 'tada hankali' game da damfara da ayyukan laifi da ake yi wurin biyan wadanda suka yi nasara
  • Kazalika, kwamishina na al'adu, nishadantarwa da yawon bude ido, Donatus Onyeji, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa

Anambra - Gwamnatin jihar Anambra ta bada umurnin dakatar da dukkan gidajen caca wato casina da gidajen wasan gyam a jihar.

A cewar The Punch, an bada wannan umurnin ne bayan samun rahoton ayyukan damfara da laifuka a wuraren.

Soludo
Gwamna Soludo Ya Rufe Dukkan Gidajen Caca Da Wasanni A Jiharsa, Ya Bada Dalili Mai Karfi. Hoto: Charles Chukwuma Soludo.
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

An Samu Jihar Farko a Arewa da ta fara Cin Dukiyar Fetur Bayan Gano Danyen Mai

Gwamna Soludo ya tabbatar da umurnin

Wannan umurnin na cikin wata sanarwa ne mai dauke da sa hannun kwamishinan Al'adi, Nishadi; Yawon Bude Ido, Donatus Onyenji da Shugaban, Hukumar karbar harajin jihar Anambra; Richard Madiebo da Kwamishinan harkokin cikin gida, Chikodi Angra.

Sun yi ikirarin cewa gwamnati ta samu rahoto mai tada hankali da ya shafi yadda ake magudi a na'urorin gidan caca da rashin gaskiya wurin biyan wadanda suka ci cacan.

A cewar sanarwar, zargin karan tsaye ne ga tsarin aiki na kasashen duniya a bangaren wanda gwamnatin Farfesa Chukwuma Soludo ba za ta lamunta ba.

Ta ce gwamnatin jihar Anambra ba za ta amince da ayyukan damfara ba a karkashin gwamnati mai ci a yanzu.

An Haramta Amfani Da 'Mini Skirt' A Matsayin Unifom A Makarantun Wata Jihar Kudancin Najeriya

Gwamnatin Jihar Anambra ta haramta saka gajerun siket wato 'mini skirt' a matsayin unifom a dukkan makarantun jihar, Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Halaka Dan Sanda Da Wasu 22 Sannan Suka Kona Gidaje 50 A Wata Jahar Arewa

Kwamishinan Ilimi na Jihar, Farfesa Ngozi Chuma-Udeh, ne ta bayyana hakan a Awka a ranar Lahadi tana mai cewa sanarwar haramcin ya zama dole domin makarantu za su dawo hutu a ranar Litinin.

Ta ce tuni an sanar da sakatarorin ilimi na makarantun gwamnati da masu zaman kansu game da dokar haramcin.

Kungiyar Musulunci, MURIC, Ta Yi Martani Kan Haramta Saka 'Mini Skirt' A Makarantun Jihar Anambra

A wani rahoton, kungiyar musulunci ta MURIC ta yaba wa Gwamna Charles Soludo na Jihar Anambra kan haramta saka gajerun sket wato 'mini skirt' a makarantun mata na gwamnati da masu zaman kansu a jihar.

MURIC ta ce haramtawar ya yi daidai da neman yancin saka hijabi da kungiyoyin musulmi ke yi a Najeriya, Nigerian Tribune ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel