Jerin Sunaye da Kudin da Manyan Attajiran Afrika 5 Suka Tara a Watan Oktoba

Jerin Sunaye da Kudin da Manyan Attajiran Afrika 5 Suka Tara a Watan Oktoba

  • A cikin kwanaki 30 da suka gabata, manyan masu kudi sun ga yadda dukiyoyinsu suka yi kasa ko kuma suka tumbatsa
  • A jerin biloniyoyin da Bloomberg suka fitar, manyan attajiran Afrika sun fuskanci cigaba da yalwar dukiyoyinsu
  • A cikin jerin attajiran, an ga Aliko Dangote na Najeriya yayi zaman dirshan a matakin farko yayin da ‘yan Afrika ta Kudu suka cika jerin

A kwanaki 30 da suka gabata, Elon Musk, babban attajiran duniya yayi asarar $39 biliyan sakamakon faruwar farashin Tesla.

Har a halin yanzu zaune yake daram a matsayin mutumin da yafi kowa kudi a duniya.

Attajiran Afrika
Jerin Sunaye da Yadda Manyan Attajiran Afrika 5 Suka Tara Dukiyarsu. Hoto daga Bloomberg/Contributor
Asali: Getty Images

Kamar yadda Bloomberg suka bayyana, manyan attajiran Afrika basu girgiza ba yayin da aka samu sauyi a arzikinsu a watan Oktoban 2022.

Wannan jerin ya duba hawa da saukar arzikinsu da kuma ribar da ake samu a kasuwacinsu wanda yake nuna nawa ake rasawa ko ake samu tun farkon wannan shekarar.

Kara karanta wannan

Cin Bashi Don Gudanar Ayyukan Cigaba Ba Laifi Bane: Cewar Bankin CBN

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aliko Dangote: $18.5bn

Aliko Dangote har yanzu shine zaune daram kuma dirshan a sahun gaba matsayin mutumin da yafi kowa arziki a Afrika inda arzikinsa ya kai $18.5bn.

Ribar da ya samu daga farkon shekarad nan zuwa yanzu ta kai N572 miliyan kuma asarar da ya tafka ta kai $64.4 miliyan.

Johann Rupert da iyalansa: $8.71bn

Iyalan Rupert sune na 206 a jerin biloniyoyin duniya da Bloomberg suka fitar. ‘Yan asalin Afrika ta kudun sun mallaki $8.71 biliyan.

Daga farkon shekarar nan zuwa yanzu sun samu ribar $3.24 biliyan.

Nicky Oppenheimer: $7.93bn

Oppenheimer a yanzu yana da kudi da suka kai $7.93 biliyan. Attajirin mai hakar ma’adanai na kasar Afrika ga kudun yayi asarar $75 miliyan. Daga farkon shekarar nan zuwa yanzu ya samu ribar $25 miliyan kuma yana mataki na 237 na masu kudin duniya.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Budewa Masu Bauta Wuta, Sun Halaka 2 tara da Jigata Wasu a Kogi

A watan Yuni, Oppenheimer yafi Rupert da Johann arziki kuma shi ne na biyu a jerin masu kudin Afrika.

Nathan Kirsh: $7.21bn

‘Dan kasuwan asalin ‘dan kasar Afrika ta kudun yana da dukiya da ta kai $7.21 biliyan. Ya samu ribar da ta kai $64.5 miliyan.

Daga farkon shekarar nan zuwa yanzu ya samu $1.06 biliyan kuma yana mataki na 273 na jerin masu kudin duniya. Shi ne na 8 a jerin masu kudin Afrika.

Nassef Sawiris: $6.44bn

Biloniyan ‘dan asalin kasar Misra yana da dukiya mai darajar $6.44 biliyan. A baya bayan nan ya tafka asarar da ta kai $152 miliyan. A yanzu shi ne na 320 cikin mashahuran attajiran duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel