EFCC Ta Kama Jami'in EFCC Na Bogi Bayan Ya Damfar Yar Kasar Waje N19m, Hotuna Sun Bayyana

EFCC Ta Kama Jami'in EFCC Na Bogi Bayan Ya Damfar Yar Kasar Waje N19m, Hotuna Sun Bayyana

  • Jami'an EFCC sun kama wani Ume Ifechukwu Clinton kan damfarar wata yar kasar Belgium, Axeller Mahire €45,000 (N19.2 million)
  • Clinton ya tuntube yar Belgium din a shekarar 2021 a Facebook, inda ya yi ikirarin shi ma'aikacin EFCC ne
  • An kama dan shekara 29 a Legas, a ranar Talata, 18 ga watan Oktoba, bayan rahoto a kafafen watsa labarai cewa ya damfari Mahieu

Legas, Najeriya - Jami'an hukumar yaki da rashawa ta EFCC sun kama wani dan shekara 29 mai suna Ume Ifechukwu Clinton saboda sojan gona, damfara ta kwamfuta da karbar kudi ta hanyar karya da almundahar kudi.

Wata sanarwa da hukumar yaki da rashawar ta fitar a ranar Alhamis, 20 ga watan Oktoba ya nuna cew an kama Clinton ne a ranar Talata, 18 ga watan Oktoba, a gida mai lambar 46 Atoke Gbadebo Street, Isheri, Legas.

Kara karanta wannan

Jami'in Soja Ya Arce Da Kudin Kwamanda N36m A Jihar Rivers, An nemesa an rasa

EFCC Na Bogi
EFCC Ta Kama Jami'in EFCC Na Bogi Bayan Ya Damfar Yar Kasar Waje N19m, Hotuna Sun Bayyana. Hoto: Hukumar EFCC
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Legit.ng ta tattaro cewa jami'an na EFCC sun kama shi ne bayan rahoto a kafar watsa labarai kan yadda Clinton ya damfari Axelle Mahieu, malama da ke aiki a matsayin mai bada kulawa a Brussels, Belgium.

Jami'in EFCC na bogi: Yadda Clinton ya damfari Mahieu

Mahieu tana amfani da shafinta na Facebook ne a Nuwamban 2021 sai ta ga sako daga Clinton, yana gabatar da kansa a matsayin abokin abokinta.

Da suka cigaba da tattaunawa bayan kwanaki, Clinton ya fada wa Mahieu cewa shi jami'in EFCC ne kuma ya nuna mata katin shaida na bogi.

Bayan watanni da dama suna hirar waya ta bidiyo kuma ya samu Mahieu ta amince da shi, Clinton ya mata tayin kasuwancin Crypto tare da alkawarin za ta samu riba sosai kuma ba abin da zai samu uwar kudin ta.

Kara karanta wannan

Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Kasa a APC Ya Jingine Tinubu, Ya Faɗi Wanda Yake So Ya Gaji Buhari a 2023

Bayan ta amince da shi, Clinton ya damfare ta har na €45,000 kimanin N19.2 miliyan.

Kama Ifechukwu Clinton: Yan Najeriya sun yi martani

Tajudeen Bhadmus ya ce:

"Ku kwace dukkan kudin daga hannunsu ku tura shi gidan gyaran hali na shekaru 15 ya koyi hali mai kyau da hakuri."

Falagbo Emmanuel ya ce:

"Wannan zamanin na Soshiya Midiya, dole a yi takatsantsan. Amma doka za ta kai ga kowa."

Rilwan Ahmed ya ce:

"Mutane na da karfin hali."

Matthias Umenyili ya ce:

"Laifi ba shi da amfani, Allah ya kiyaye."

Hukumar EFCC Ta Kama 'Yahoo Boys' 41 Da Dukiyoyin Da Suka Mallaka

A wani rahoton, hukumar hana almundahana da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFC ta cika hannu da yan damfarar yanar gizo wanda aka fi sani da Yahoo Boys 41.

Matasan 'Yahoo Boy' sun shahara da sace kudaden mutane ta manhajojin bankin wayansu da kuma yanar gizo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel