Jami'in Soja Ya Gudu Da Kudin Kwamandan N36m A Jihar Rivers

Jami'in Soja Ya Gudu Da Kudin Kwamandan N36m A Jihar Rivers

  • An nemi jami'in Soja an rasa bayan kwashe kudin kwamandansa kusan milyan 40 a jihar Rivers
  • Hukumar Sojin Ruwan Najeriya ta ce lallai ya gudu daga aiki amma babu labarin guduwa da kudi
  • Majiyoyi sun bayyana cewa shi kansa Kwamandan kudin rashawa ce ya tara aka sace

Wani jami'in Soja dake aiki a Hydrocarbon Pollution Remediation Project, HYPREP, a Port Harcourt, mai suna O. Badamasi, ya arce da kudin kwamandansa N39million a Rivers.

DailyNigerian ta ruwaito cewa Sojan ya ajiye rigar Sojarsa, bindiga da katin shaidan zaman Soja kuma ya gudu da kudaden.

Rahoton ya kara da cewa Kwamandan na HYPREP, Izokpu Ose, bai son labarin ya yadu saboda shi kansa kudin rashawa ce ya tara.

Kara karanta wannan

Duk Jam'iyyar Dake Takara Da APC a Legas 'Batawa Kanta Lokaci Take, Wike

Majiya ta bayyana cewa Kwamandan dai ya tafi jihar Legas don ganawa da iyalan Sojan domin su gargadesa ya dawo masa da kudinsa.

Izokpu
Jami'in Soja Ya Gudu Da Kudin Kwamandan N36m A Jihar Rivers Hoto: DailyNigerian
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar majiyar:

"Ya je Bonny Island da Warri domin neman Sojan amma an nemeshi an rasa."

A cewar DailyNigerian, Wata majiyar ta bayyana mata cewa an dade ana zargin Kwamanda Izokpu da rashawa da zalunci a HYPREP.

Majiyar tace kwamandan na karban milyan 21 a wata kudin ma'aikata amma milyan 15.3m kadai yake biya, shi ya handame N5,850,000

Tace:

"Kwamanda Izokpu na ikirarin cewa Sojoji 141 ke aiki tare da shi, alhali mutum 102 ne - Sojin ruwa 30, Mopol 17, CTU 16, Sojin kasa 5, da Sibil Defence 20."
"Ana bashi N8,460,000 kudin RCA a wata, amma N6,120, 000 yake biyan jami'an. Shi ke rike sauran N2,340,000"

Kara karanta wannan

Jigon PDP: Mun daina aikata zunubi saboda Atiku ya lashe zaben 2023

"Yana ikirarin motocin hilux 20 yake haya daga wajen Bariki amma motoci uku kadai muka gani."
"Sauran kudin hayar Hilux N12,750,000 zai zuba a aljihu. Haka yake yi tun Mayun 2021."

Kakakin hukumar Sojin ruwan Najeriya, Adedotun Ayo-Vaughan, ya tabbatar da labarin cewa lallai Soja O Badamasi ya gudu amma basu samu labarin ya gudu da kudi ba.

Yace:

"Sojan ruwan ya ajiye aiki ya gudu, ya dade da tafiya ba tare da izini ba amma bai gudu da kudin kwamandan ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel