Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa a APC Ya Jingine Tinubu, Ya Koma Bayan Obi a 2023

Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa a APC Ya Jingine Tinubu, Ya Koma Bayan Obi a 2023

  • Wani ɗan takara da ya nemi tikitin shugaban kasa a APC a 2019 ya ayyana goyon bayansa ga Peter Obi na jam'iyyar LP
  • Charles Udeogaranya, yace takara Musulmi da Musulmi da APC ke kokarin ƙaƙabawa yan Najeriya wata makarkashiya ce
  • Yace lokaci ya yi mutanen kasa zasu jingine kowane banbanci su zabi wanda ya cancanta da shugabancin ƙasar nan

Abuja - Tsohon ɗan takarar da ya nemi tikitin shugaban kasa a inuwar APC a 2019, Charles Udeogaranya, ya ayyana goyon bayansa ga Peter Obi na jam'iyyar Labour Party.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Mista Udeogaranya ya tabbatar da mara wa Obi baya ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, 18 ga watan Oktoba, 2022 a Abuja.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wasu Sabbin Hotuna Daga Aso Villa Sun Nuna Tinubu Na Kus-Kus da Mataimakin Buhari

Peter Obi
Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa a APC Ya Jingine Tinubu, Ya Koma Bayan Obi a 2023 Hoto: punchng
Asali: UGC

Yace tikitin Musulmi da Musulmi da tsohuwar jam'iyyarsa APC ta zaɓa wata alama ce ta shirin canza Najeriya zuwa ƙasar Musulunci.

Mista Udeogaranya ya ayyana tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, a matsayin ɗan takara mai nagarta da ya cancanci ya jagoranci Najeriya kuma ya tsamo ta daga ramin da ta auka.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Legit.ng Hausa ta gano cewa wannan na zuwa ne watanni uku kacal bayan wani ɗan takarar APC, Dr. S.K.C. Ogbonnia, ya janye daga goyon bayan Bola Tinubu, kana ya fito fili ya sanar da koma wa gidan Obi a 2023.

Meyasa ya goyi bayan takarar Peter Obi?

A sanarwar ranar Talata, Udeogaranya, yace yana takaicin yadda 'yan Najeriya ke ganin abinda ake kira, "Tangal-tangal na tattalin arziki," wanda ya haddasa fargaba a zuƙatan yan kasa.

Kara karanta wannan

Ziyarar da Peter Obi Ya Kai wa Dr. Ahmad Gumi ta Jawo Masa Bakin jinin Magoya baya

Yace:

"Akwai bukatar wayar da kai domin tikitin Musulmi da Musulmi da APC ke shirin ƙaƙabawa yan Najeriya wata alama ce ta maida ƙasar ta Musulunci. Lallai ne tikitin da waɗanda aka tsayar ba su da abinda zasu wa Najeriya."
"Duba da haka, Ni Chief Charles Udoka Udeogaranya, ina goyon bayan ɗan takarar LP, Peter Obi, domin ya cancanta ya ja ragamar al'amuran Najeriya."

A wani labarin kuma Bidiyon Abinda Ya Faru Yayin da Tinubu da Atiku Suka Haɗu a Filin Jirgin Sama

Manyan yan takarar shugaban ƙasa biyu dake sahun gaba, Bola Tinubunda Atiku Abubakar sun haɗu a filin jirgin sama a Abuja.

Bayanai sun nuna cewa jiga-jigan siyasar biyu sun gaisa da juna yayin da yan tawagarsu ke kiran sunan iyayen gidansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel